--
Yanzu yanzu: COVID-19: Jamus ta sake bawa Najeriya tallafin N2.2bn

Yanzu yanzu: COVID-19: Jamus ta sake bawa Najeriya tallafin N2.2bn



Kasar Jamus ta sake sanar da cewa za ta bawa Najeriya tallafin kudin Fam miliyan 5.5 domin taimaka mata yaki da annobar Coronavirus a kasar kamar yadda The Punch ta ruwaito. Jamus ta sanar da hakan ne ta shafin ta na Twitter @GERinNigeria a ranar Talata inda ta ce a wannan karon za ta bayar da tallafin €5.5 domin tallafawa gajiyayyu a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Sanarwar ta ce, "Jamus ta sake bayar da Fam miliyan 5.5 (N2.2bn) ga asusun tallafin Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya ke kula da shi domin cigaba da ceto rayukan mutanen da ke jihohin Borno, Adamawa da Yobe sakamakon annobar COVID-19.

"Ayyukan da ake yi a yankin sun hada da haka rijiyoyin burtsatse, gina ban dukuna, gyaran gidajen mutanen da suka rasa muhallinsu sakamakon rikicin Boko Haram.

"Hakan ya nuna cewa gudunmawar da Jamus ta bawa Najeriya ya kai Fam miliyan 29 tun bude asusun tallafin na NHF a Mayun 2017, wanda haka ke nuna cewa Jamus ce kasar da tafi bawa Najeriya tallafi cikin shekaru uku da suka gabata." Kasar ta kuma yi alkawarin bayar da tallafin Fam miliyan 12 ga Kungiyar Lafiya ta Kasashen Afirka ta Yamma da ECOWAS domin sayan kayan asibiti,

horas da maaikatan lafiya da sauransu a kasashen da annobar ta shafa. Ta kara da cewa za ta bawa Rundunar Yan Sandan Najeriya gudunmawar kayyaki da suka hada da man kashe kwayoyin cuta, takunkumin fuska, safar hannu da sauransu da kudinsu ya Fam 20,000. Za a mika wa rundunar yan sandan kayan ne a birnin tarayya Abuja. A cewar hukumar NCDC, an samu mutum 41 masu COVID-19 a Borno, daya a Adamawa yayin da jihar Yobe kuma har yanzu babu mai dauke da cutar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Related Posts

0 Response to "Yanzu yanzu: COVID-19: Jamus ta sake bawa Najeriya tallafin N2.2bn"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?