
Yanzu-yanzu: Buhari ya saka dokar hana fita na tsawon makonni biyu a jihar Kano
Monday, 27 April 2020
Comment
Yace: "Game da Kano, na bada umurnin kafa dokar hana fita gaba daya na tsawon makonni biyu fari daga yanzu." "Gwamnatin tarayya za tayi dukkan iyakan kokarinta na kudi, kayan aiki da ma'aikata wajen taimakawa jihar wajen takaita yaduwar cutar a jihar da kuma zuwa wasu jihohin dake makwabta."
BEHIND THE SCENE: President Muhammadu Buhari's Broadcast to the Nation, aired on NTA and other local television stations earlier today. pic.twitter.com/TSN57Qy0iQ— Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) April 27, 2020
A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita dokar hana fitar da ya kakabawa al'ummar birnin tarayya Abuja, jihar Legas da Ogun, da tsawon mako daya. Shugaban kasan ya sanar da hakan ne a jawabin da yayi ga yan kasa karo na uku kan lamarin annobar Korona. Yace:"Dokar hana fita a FCT, Legas da Ogun zai cigaba da kasancewa zuwa ranar 4 ga Mayu, 2020." Amma daga ranar 4 ga Mayu,
Buhari ya bayyana cewa za'a fara sassauta dokar hana fitar a wadannan garuruwan. Yace: "Bisa ga shawarwarin da kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19, kwamitocin duba illan lamarin ga tattalin arzikin kasa da kungiyar gwamnonin Najeriya, na bada umurnin saukaka dokar hana fita a FCT, Legas da Ogun fari daga ranar Litnin, 4 ga Mayu, 2020."
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Yanzu-yanzu: Buhari ya saka dokar hana fita na tsawon makonni biyu a jihar Kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?