--
Yanzu-yanuz: An samu karin mutane biyu da suka kamu da Coronavirus a Kano

Yanzu-yanuz: An samu karin mutane biyu da suka kamu da Coronavirus a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa an samu karin mutane biyu da suka kamu da cutar a jihar, kwana biyu da bullar cutar a jihar. Hadimin gwamna Abdullahi Ganduje kan kafafen yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana hakan ne da yammacin Litinin. A yanzu ,

adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya zama uku. Jawabin yace: "An sake samun mutum 2 da suka kamu da cutar Corona wato Covid-19 a jihar Kano, bayan sakamakon gwajin da akayi musu wanda ya tabbatar da cewa suna da cutar, wanda ya kawo adadin masu ita a Kano suka zama 3."

Coronavirus a Kano Source: Facebook 

A bangare guda, Jami'an hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, sun shawarci tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya killace kansa bayan gwajin da akayi masa a jihar Kano.

Rahoton ya bayyana cewa hukumar NCDC ta ce hakan na cikin ka'idojin da aka kindaya ga mutanen da aka yiwa gwaji kafin sakamakon gwajinsu ya fito. Sakamakon bibiyan mutanen da mutumin farko da ya kamu cutar a Kano yayi mu'amala dasu, an gano cewa tsohon gwamna Lamido ya halarci wata jana'izar da mutumin ya halarta a Koki. Shugaban ma'aikatar kiwon lafiyan jihar Kano,

Dr. Imam Wada Bello, ya tura wasikar kar ta kwana ga Sule Lamido inda ya bukaci daukar jini da yawunsa domin gwaji. Sule Lamido da kansa ya daura wasikar a shafinsa na Facebook inda ya aka bukaci gwada shi.

Source: Legit.ng KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Yanzu-yanuz: An samu karin mutane biyu da suka kamu da Coronavirus a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?