
Yan' sanda sun kama barauniyar yara dauke da kananan yara 27 a Taraba
Monday, 6 April 2020
Comment
Missal ya ce sun ceto yaran ne daga hannun Mary a ranar Lahadi a tashar Takalma dake karamar hukumar Gassol na jahar Taraba. Daga cikin yaran dake hannunta akwai mata 13 da maza 14. Mista Misal yace tuni sun mika yara 33 da matar ta sata ga iyayensu, sa’annan sun mika sabbin yara 27 ga ma’aikatar kula da harkokin mata, yayin da suka gurfanar da matar gaban kotu. An fara kama Mary ne a ranar 26 ga watan Feburairu a garin Bali da laifin safarar yara. A lokacin da aka kamata na farko tana dauke da yara 23,
wadanda take shirin safararsu tare da cinikinsu a wani gari, ba ta dandara ba, inda aka sake kamata a ranar 4 ga watan Maris, a wannan lokaci jagoranci Yansanda zuwa mafakarta dake Mararraban Donga inda suka ceto yara 10. A wani labarin kuma, wani lamari mai ban takaici ya faru a jahar Bayelsa inda wasu zauna gari banza suka kwashe tarin kayan abinci da gwamnati tanadar ma jama’a a matsayin tallafi.
Kayan abincin da miyagun suka sace ya hada da buhunan shinkafa da buhunan Garri, haka zalika sun miyagun sun fasa wata ma’aijiyar kayan abinci a yankin Igbogene na garin Bayelsa, inda suka kwashe shinkafa da Garri. Wani shaidan gani da ido da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa miyagun sun afka wurin da ake rabon abincin ne dauke da bindigu inda suka dinga harbe harbe, wanda hakan yasa jama’a tserewa, kafa mai na ci ban baki ba.
KARANTA: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwaLATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Yan' sanda sun kama barauniyar yara dauke da kananan yara 27 a Taraba"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?