
'Yan sanda sun damke matar da tayi wa hadimarta tsarki da tozali da barkono
Thursday, 16 April 2020
Comment
- Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta damke wata tsohuwa mai shekaru 75 wacce ake zargi da duka tare da zuba barkono a ido da gaban mai aikinta - Mai aikin mai suna Chidinma ta ce an dauko ta ne daga Ohaji Egbema da ke jihar Imo kusan watanni 12 da suka gabata
- Chidinma ta sanar da jaridar The Nation cewa, matar ta saba gayyatar bata-gari don dukanta a duk lokacin da ta bata mata rai Rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi ta damke wata tsohuwa mai shekaru 75 wacce ake zargi da duka tare da zuba barkono a ido da gaban mai aikinta. Makwabtan matar mai suna Comfort Obi ne suka mika ta gaban ofishin 'yan sanda da ke Ekumenyi a Abakaliki sakamakon tsananin zaluntar mai aikinta da take yi.
Ta farfasawa mai aikin jiki sakamakon tsananin dukan da take mata. Mai aikin mai suna Chidinma ta ce, an dauko ta ne daga Ohaji Egbema da ke jihar Imo kusan watanni 12 da suka gabata. An kaita wajen Comfort Obi ne don tayata ayyukan gida kuma ana biyanta. Bincike ya nuna cewa, Chidinma ta fara aikatau ne bayan mutuwar mahaifiyarta da makantar mahaifinta wanda nauyin 'yan uwanta hudu yake kansa. Chidinma ta sanar da jaridar The Nation cewa, matar ta saba gayyatar bata-gari don dukanta a duk lokacin da ta bata mata rai.
Ta ce a duk lokacin da ta dauka biskit da ruwan lemu na matar bayan ta barta da yunwa, tana watsa mata barkono a gabanta da idanunta. Osita Ezechukwu makwabcinsu ne wanda ya garzaya ofishin 'yan sanda don gudun kada ayi kisan kai a kusa dasu. Ya ce ba sau daya ba ya ke jan kunnen matar a kan ta gujewa cin zarafin mai aikin. Ya ce baya ga duka, tana ba mai aikin aiki mai matukar wahala.
Matar tace duk da tayi nadamar abinda tayi, sai da ta nemi izinin kanwar mahaifin mai aikin kafin ta watsa mata barkono a gaba. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi, Loveth Odah ta tabbatar da aukuwar lamarin. Ta ce an bayar da belin wacce ake zargin, ita kuwa mai aikin an dubata a asibiti tare da mika ta ga iyayenta. Ta kara da cewa za a gurfanar da wacce ake zargin bayan annobar Coronavirus ta wuce.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "'Yan sanda sun damke matar da tayi wa hadimarta tsarki da tozali da barkono "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?