
Yadda annobar covid-19 ta hallaka mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya
Sunday, 26 April 2020
Comment
Annobar cutar covid-19 ta hallaka Francis Bissong, mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya mai kula da sashen binciken manyan laifuka, a jihar Edo. Bissong, babban jami'in dan sanda, ya mutu ne a gidansa da ke birnin Benin a ranar Talatar da ta gabata. Duk da kwamishinan yada labarai na jihar Edo, Patrick Okundia, ya sanar da mutuwar Bissong, amma bai yi karin bayani a kan mutuwar ba.
Paul Yakadi, mataimakin shugaban rundunar 'yan sanda na shiyya ta 5 da ke Benin, ya fitar da cikakken bayani a kan mutuwar Bissong, wanda ya bayyana da 'hazikin dan sanda'. Yakadi ya ce a ranar 9 ga watan Afrilu ne marigayi Bissong ya yi bulaguro zuwa Akure, babban birnin jihar Ondo, domin yin bikin ista tare da iyalinsa. Ya dawo Benin bayan ya shafe kwanaki biyar a Akure, kuma bayan dawowarsa ne ya yi korafin cewa yana fama da zazzabi mai zafi, lamarin da ya sa shi killace kansa.
"An dauki jininsa a ranar 18 ga watan Afrilu domin gudanar da gwaji, inda kuma sakamakon gwajin ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar covid-19," a cewar jawabin da Yakadi ya fitar. Jawabin Yakadi ya cigaba da cewa; "nan da nan muka tuntubi ma'aikatan hukumar shawo kan cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) domin su zo su dauke shi zuwa cibiyar killacewa, amma kafin su zo ya mutu, sai gawarsa su ka zo su ka samu."
Kazalika, Yakadi ya yi watsi da rahotannin da suka bayyana cewa Bissong ya mutu ne a wani asibitin rundunar 'yan sanda da ke Benin. "Domin kore duk wani shakku, zan sake maimaita cewa marigayi Bissong ya mutu ne a gidansa da ke rukunin gidajen manyan jami'an 'yan sanda da ke daf da hedikwatar 'yan sanda shiyya ta 5 da ke birnin Benin," a cewarsa. Dukkan wasu jami'an 'yan sanda da suka yi mu'amala da marigayi Bissong sun killace kansu, yayin da aka saka maigadinsa, direba da sauran hadimasa a karkashin kulawa ta musamman.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Yadda annobar covid-19 ta hallaka mataimakin kwamishinan 'yan sandan Najeriya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?