
Wata sabuwa: Gwamna ya raba ma matasa barasa don maganin cutar Coronavirus
Thursday, 16 April 2020
Comment
Gwamna Sonko ya raba kwalaben giyan ne tare da kayan abinci ga talakawa, inda aka hange shi yana sanya kwalaben giyan cikin kayan abincin da ya raba ma jama’a. A cewarsa, manufar raba kayan abincin shi ne domin rage ma talakawa radadin mawuyacin halin da suke ciki a sanadiyyar bullar annobar Coronavirus mai toshe numfashin dan Adam.
“Muna hadawa da kwalaben giya ne a cikin kayan abincin da muke raba ma jama’an mu, bincike na cibiyar lafiya ta duniya, WHO, da sauran kungiyoyin kiwon lafiya ya nuna giya na taka muhimmin rawa wajen magance Coronavirus.” Inji shi.
Gwamna Sonko Source: Facebook Sai dai kamfanin LVMH dake hada giyan ta musanta Gwamna Sonko, inda tace: “Shan giyan mu ko wani iri ne baya maganin kamuwa da Coronavirus ko kuma ya yi maganinta, muna kira ga jama’a su wanke hannuwansu a akai akai don kare kansu daga cutar.” Kaakakin gwamnatin kasar, Cyrus Oguna yace babu wani binciken kimiyya da ya nuna giya na maganin Coronavirus,
don haka ya gargadi yan siyasa da su kauce ma neman suna da cutar. Kasar Kenya na da mutane 225 da suka kamu da cutar, kuma tuni ta takaita zirga zirgan jama’a don rage yaduwar cutar, amma gwamnati da masu kudi na taimaka ma jama’a da abinci. Ita dai cutar Coronavirus na bukatar matakan kandagarki ne a yanzu sakamakon ba ta da magani, sai dai kuma ana iya kara karfin garkuwan jiki domin yaki da cutar idan ta shiga jiki. Kamar yadda yan Hausa ke fadi idan kana da kyau sai ka kara da wanka, ga wasu daga cikin hanyoyin karfafa garkuwan jiki domin ya yaki cututtuka yayin da suka shiga jikin dan Adam;
- Kauce ma shan taba da sauran kayan hayaki - Cin abinci mai kayan ganye - Motsa jiki a kai a kai KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Wata sabuwa: Gwamna ya raba ma matasa barasa don maganin cutar Coronavirus "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?