--
Wani ya harbe mutum 5 saboda sun dame shi da surutu

Wani ya harbe mutum 5 saboda sun dame shi da surutu

Wani mutum a kasar Rasha ya harbe mutum biyar saboda sun dame shi da surutu a kofar gidansa da dare.

'Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne a kauyen Yelatma da ke yankin Ryazan mai nisan kilomita 200 daga kudu maso gabashin birnin Moscow.

Yankin yana killace saboda annobar coronavirus da ake fama da ita.

Bincike ya nuna cewa mutumin ya gargadi mutanen daga barandar benensa. Nan take hayaniya ta barke tsakaninsu kuma ya bude musu wuta da wata bindigar farauta.

Maza hudu da mace daya sun mutu nan take sakamakon raunin da suka ji da karfe 10:00 na daren Asabar, a cewar kwamitin da ke binciken lamarin.

An kama wanda ake zagin da ba a bayyana sunansa ba. An bincika gidansa kuma aka kwace bindigar tasa.
LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Wani ya harbe mutum 5 saboda sun dame shi da surutu"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?