
Tirkashi: Bidiyon yadda wani saurayi ya zabge wani soja da mari ya gudu saboda ya dake shi
Friday, 3 April 2020
Comment
Duk da dai ba a bayyana ainahin abinda ya saka sojan yake yi musu hukuncin ba, mutumin ya ranta ana kare yayin da sojan yaja da baya yake kokarin harbin shi da bindiga sakamakon marinsa da mutumin yayi.
Wani wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook mai suna Abdul Waris, ya sanar da cewa lamarin ya faru ne a Old Tafo cikin garin Kumasi dake kasar Ghana, a lokacin da kasashe da dama suka hana mutane fita daga gida saboda annobar Coronavirus.
Sai dai wannan din bashi da nasaba da hana fita, domin kuwa mutane da dama suna ta zirga-zirga a lokacin da lamarin ya faru.
Ga dai bidiyon yadda lamarin ya kasance:
0 Response to "Tirkashi: Bidiyon yadda wani saurayi ya zabge wani soja da mari ya gudu saboda ya dake shi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?