--
Tashin hankali: Wani dan Najeriya mai Coronavirus ya gantsarawa ma'aikaciyar jinya cizo a fuska

Tashin hankali: Wani dan Najeriya mai Coronavirus ya gantsarawa ma'aikaciyar jinya cizo a fuska



Jami'an tsaro sun garkame wani dan Najeriya mai fama da cutar Coronavirus kan laifin gantsarawa wata ma'aikaciyar jinya yar kasar Sin cizo a fuska don ta hanashi guduwa daga inda aka killaceshi. Mutumin mai suna Okonkwonwoye Chika Patrick ya doki matar ne saboda bayan ta hanashi fita daga asibitin dake Guwangzhou. Faifan bidiyon ya nuna yadda ma'aikaciyar jinyar tana fashewa da kuka tana nuna wuraren da ya ji mata rauni.

Tashin hankal Source: Facebook

Yayinda ta bukaci daukar jininsa domin yin gwaji ranar 1 ga Afrilu, Okonkwonwoye yayi banza da ita kuma ya nufi fita daga dakin killacewar. Yayinda tayi kokarin tareshi daga fita, sai ya ture ta kasa, ya cijeta a fuska. Jami'an yan sanda sun garkameshi kuma yana cigaba da jinya karkashin lurar yan sanda. Za'a hukuntashi bisa dokokin kasar Sin lokacin da ya samu lafiya.

Dan Najeriyan, Okonkwonwoye Chika Patrick, ya kasance a asibitin tun ranar 23 ga Maris, 2020. Ya kamu da cutar Coronavirus bayan komawa garin Guangzhou ranar 20 ga Maris.

Kalli bidiyon ma'aikaciyar jinyar:
               

 A nan gida kuwa, Mazauna unguwar Narayi a garin Kaduna sun yi wawason kayan abincin da aka ajiye da niyyar raba wa marasa karfi a unguwa a suka bar yan kwamitin da aka daura wa alhakin rabon kayan abincin sun kallonsu babu yadda za su yi da su.

KARANTA:Wadume: Kotu ta umurci Buratai da ya mika sojoji da ke cikin lamarin don gurfanar dasu

Kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ne ta bayar da kayayyakin abincin domin a raba wa talakawa yayin da suke zaune a gidajensu sakamakon dokar hana fita da aka saka saboda coronavirus. Shugaban kwamitin rabon, Malam Sule Garba ya ce lamarin ya afku ne a ranar Litinin da yamma a makarantar frimari ta LEA da ke Narayi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Garba wanda kuma shine mai unguwar ta Narayi,

ya shaidawa NAN a ranar Talata a Kaduna cewa dandazon matasa maza da mata sun suke wawushe kayin abincin suka tsere.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Tashin hankali: Wani dan Najeriya mai Coronavirus ya gantsarawa ma'aikaciyar jinya cizo a fuska "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?