
Shugaban kwamitin yaki da Coronavirus a Kano ya kamu da cutar
Friday, 17 April 2020
Comment
Farfesa Habib na daga cikin mutane 12 da hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, ta fitar da sakamakon gwajin da ta musu a ranar Laraba, 16 ga watan Afrilu, inji rahoton Vanguard.
Wata majiya ta tabbatar da lamarin, inda ta ce: “Da gaske ne, kuma abin takaici, Farfesa Habib ya kamu da COVID-19, a yanzu haka an kwantar da shi a cibiyar killacewa dake Kwanar Dawaki.”
Farfesa Habib kwararren likita ne da ya goge a kan sha’anin cututtuka masu yaduwa, kuma shi ne shugaba na biyu a kwamitin yaki da COVID-19 ta jahar Kano da Gwamna Ganduje ya kafa.
Wani babban memba a kwamitin ya bayyana cewa Farfesan ya kamu da cutar ne yayin da yake kulawa da wasu daga marasa lafiya dake dauke da cutar ta Coronavirus a jahar Kano.
Kazalika Farfesan babban malami ne a jami’ar Bayero, inda yake koyar da yadda za’a iya sarrafa garkuwan jikin dan Adam domin yaki da cututtuka kamarsu sida, cizon maciji da sauransu.
Duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin kwamishinan kiwon lafiya na Kano, Aminu Ibrahim Tsanyawa game da lamarin ya ci tura sakamakon bai amsa sakon da ta tura masa ba.
A ranar 21 ga watan Maris ne Ganduje ya nada kwamitin a karkashin jagorancin mataimakin gwamna Nasiru Yusuf da Farfesa Habib da nufin su dakile yaduwar cutar Covid-19 a Kano.
Ita dai cutar Coronavirus na bukatar matakan kandagarki ne a yanzu sakamakon ba ta da magani, sai dai kuma ana iya kara karfin garkuwan jiki domin yaki da cutar idan ta shiga jiki.
Kamar yadda yan Hausa ke fadi idan kana da kyau sai ka kara da wanka, ga wasu daga cikin hanyoyin karfafa garkuwan jiki domin yaki da cututtuka yayin da suka shiga jikin dan Adam;
- Kauce ma shan taba da sauran kayan hayaki
- Cin abinci mai kayan ganye
- Motsa jiki a kai a kai
- Rage kiban da ya wuce hankali
- Samun isashshen barci
- Tabbatar da tsaftar jiki da gabbai
- Rage damuwa a raiKARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN๐๐๐ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐๐๐
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Shugaban kwamitin yaki da Coronavirus a Kano ya kamu da cutar"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?