Shugaban kasar Najeriya ya yi wa Enahoro, Alli, Effiong da wasu Sojoji afuwa
Thursday, 9 April 2020
Comment
Shekaru da dama bayan mutuwarsu, gwamnatin tarayyar Najeriya ta yafewa Farfesa Ambrose Alli da Cif Anthony Enahoro a rana daya da aka yi wa wasu da ke gidan yari afuwa. Ministan harkokin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya sanar da wannan mataki da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dauka a yau Ranar 9 ga Watan Afrilu, 2020. Ga jerin wadanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa afuwar bayan sun bar Duniya:
1. Anthony Enahoro Cif Anthony Enahoro ya na cikin wadanda su ka taimaka wajen karbowa Najeriya ‘yanci. Enahoro ‘Dan siyasa ne tun jamhuriya ta farko. A 1962 aka kama shi da wasu ‘Yan siyasar AG da laifin kitsa kifar da gwamnatin Abubakar Tafawa-Balewa, wannan ta sa Enahoro ya tsere daga Najeriya. Anthony Enahoro ya rike Ministan sadarwa da kwadago da kuma Ministan harkokin na musamman a gwamnatin Sojan Yakubu Gowon. Da su aka kafa jam’iyyar NPN, ya rasu a 2010.
2. Ambrose Alli Farfesa Ambrose Folorunsho Alli Farfesan Likita ne wanda ya zama gwamna tsakanin 1979 zuwa 1983 a jihar Bendel. Bayan Janar Muhammadu Buhari ya yi juyin-mulki, ya kama gwamnan da laifin satar kudin kwangila, wannan ya sa ya yanke masu daurin shekaru 100 a kurkuku.
Buhari ya yafewa na hannun-daman Awolowo bayan shekaru 58 Source: Twitter
3. Lt. Col. Moses Effiong Laftanan Kanal Moses Effiong ya na cikin manyan Sojojin da aka samu da laifin yunkurin yi wa gwamnatin Ibrahim Babangida juyin mulki a 1986. Moses Effiong wanda ainihinsa mutumin Kuros Riba ne ya na cikin wadanda ake yankewa hukuncin kisa tare da Janar Mamman Vatsa. A gidan kurkukun Kano aka ajiye Moses Effiong har ya yi ta fama da rashin lafiya.
Sauran wadanda aka yankewa hukunci tare da shi sun hada da Chris Oche, Mike Iyorshe, Martin Luther, Asen Ahura; Daniel Bamidele, Akwashiki, V.E. West, Jonathan India Garba da wasu Sojoji uku. Sauran wadanda gwamnatin Najeriya ta yi afuwa a wannan rana su ne: Major E.J. Olanrewaju da kuma Ajayi Olusola Babalola, dukkansu sun gito ne daga Yankin Kudu maso Yammacin kasar.KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN๐๐๐ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐๐๐https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Shugaban kasar Najeriya ya yi wa Enahoro, Alli, Effiong da wasu Sojoji afuwa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?