
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a Bauchi zai yi tafsirin azumin bana
Wednesday, 15 April 2020
Comment
- Ana ganin wannan mataki da malamin ya dauka baya rasa nasaba da barkewar annobar coronavirus wacce ta addabi duniya baki daya Babban malamin nan na addinin Musulunci kuma Shugaban darikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, ya bayyana cewar a jahar Bauchi zai gudanar tafsirinsa na azumin wannan shekarar. An dai saba gudanar da tafsirin nasa ne a garin Kaduna tsawon shekara da shekaru.
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a Bauchi zai yi tafsirin azumin bana Source: Facebook
Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau Laraba, 15 ga watan Afrilu, a garin Bauchi, jaridar Leadership ta ruwaito. Sai dai ana ganin wannan mataki da malamin ya dauka baya rasa nasaba da barkewar annobar coronavirus wacce ta addabi duniya baki daya.
A wani rahoton, mun ji cewa kwamitin Masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna ta yanke shawarar dakatar da gudanar da tafsirin Al-Qur’ani mai girma kamar yadda aka saba yi a cikin Masallacin. Fitaccen Malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi ne yake gudanar da tafsiri a Masallacin a duk lokacin azumin watan Ramadana,
amma an samu sauyi a azumin bana saboda COVID-19. Babban limamin Masallacin, Farfesa Muhammad Sulaiman Adam ne ya bayyana haka, inda yace a bana Malam Ahmad Gumi zai gudanar da tafsirin ne daga wani wuri na daban. Sulaiman yace Malam Gumi ne kadai zai gudanar da Tafsirin tare da majabakinsa, kuma za’a watsa karatun a kafafen sadarwa na gani da na saurare, da shafukan sadarwar zamani.
Haka zalika, Sheikh Sulaiman ya kara da cewa Masallacin Sultan Bello zai cigaba da zama a garkame har sai lokacin da gwamnati ta bayar da izinin bude Masallatai. Daga karshe Shehin Malamin ya bayyana dalilin daukan wannan mataki shi ne don dakile yaduwar cutar, don haka ya nemi Musulmai su cigaba da addu’a domin Allah Ya yaye masifar.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a Bauchi zai yi tafsirin azumin bana "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?