
Samaila Isa ya yi fatali da mukamin ma’aikatan fadar shugaban kasa
Monday, 20 April 2020
Comment
Tsohon minista a jamhuriya ta biyu, Alhaji Sama’ila Isah Funtua ya shawarci masu danganta shi da mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da su kai kasuwa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito an ambaci Funtua mai shekaru 78 daga cikin wadanda ake sa ra zasu maye gurbin marigayi Abba Kyari wanda ya rasu a dalilin cutar COVID-19 a ranar Juma’a.
Funtua, ya taba zama jami’in mulki a Katsina NA tsawon shekaru 7, ministan ruwa, kuma yana cikin mutanen da suka tsara daftarin kundin tsarin mulki a shekarar 1994-1995.
Shi me mai kamfanin gine gine na Bulet, kamfanin mutum daya mafi girma a Najeriya da ta gina mafi kyawun gine ginen dake babban birnin tarayya Abuja, kuma babban dan jarida ne.
Don haka ya ce baya bukatar wannan muka saboda a cewarsa shi kan sa yana daukan mutane aiki a Najeriya, don haka ya girmi wani ya dauke shi aiki a wannan lokaci.
“Ni ma ina daukan ma’aikata aiki ne, don haka babu yadda za’ayi a dauke ni aiki. Ni fa minista ne a shekarar 1983, don haka wani mukami zai bani sha’awa yanzu? Na ji kunya da wata jarida ta danganta ni da wannan mukami saboda tsabar jahilci.” Inji shi.
Daga cikin wadanda da ake hasashen shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zabo sabon hadimin nasa daga cikinsu akwai gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai.
Sauran sun hada da hadimin shugaban kasa a kan harkoki na musamman, Yau Darazo, shugaban kwastam, Hamid Ali, ministan ilimi, Adama Adamu da kuma Babagana Kingibe.
A hannu gudaa, jama’a sun cigaba da bayyana kyawawan halayen marigayi Abba Kyari wanda a wasu ke ganin tamkar shi ne matsalar gwamnatin Buhari, sai ga shi ana ta wanke tas!
Shi da yake mika ta’aziyyar mutuwar Kyari, babban lauya Femi Falana ya nemi ya inganta asibitocin Najeriya da fannin kiwon lafiya a matsayin girmamawa ga marigayi Abba Kyari.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Samaila Isa ya yi fatali da mukamin ma’aikatan fadar shugaban kasa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?