--
Sabbin mutane 49 sun kamu da cutar covid-19 a Najeriya, 10 daga Kano

Sabbin mutane 49 sun kamu da cutar covid-19 a Najeriya, 10 daga Kano

A daren ranar Asabar ne hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da samun karin sabbin mutane 49 da suka kamu da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya. A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na tuwita, NCDC ta ce an samu karin sabbin mutane 23 da suka kamu da kwayar cutar Legas,

12 a Abuja da karin wasu 10 daga jihar Kano. Sauran jihohin da aka tabbatar da samun ma su dauke da kwayar cutar sun hada da jihar Ogun; mutum biyu, sai jihar Oyo da jihar Ekiti ma su mutum daya kowannensu. Samun karin mutanen 49 a ranar Asabar ya mayar da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a fadin Najeriya zuwa 542.

An sallami jimillar mutane 166 daga cibiyoyin killacewa da ke fadin kasa bayan an tabbatar da warkewarsu. Ya zuwa yanzu annobar cutar covid-19 ta hallaka mutane 19 a Najeriya, cikinsu har da shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, marigayi Abba Kyari.

KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/





LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
                            LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Sabbin mutane 49 sun kamu da cutar covid-19 a Najeriya, 10 daga Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?