
Rundunar 'yan sanda ta cafke wata mata da ke safarar makamai ga masu garkuwa da mutane
Tuesday, 14 April 2020
Comment
Fatima, wacce ta amsa laifinta da bakinta, ta bayyana cewa 'yan ta'addar na ba ta kudi masu tsoka duk lokacin da suka dawo da makamnsu bayan sun fita aiki. Ta bayyana cewa ta na boye makaman ne a cikin wani rami a gidanta, sannan ta ce ta san laifi ake aikatawa dasu. Binciken rundunar 'yan sanda ya gano cewa Fatima ta shiga wannan muguwar sana'a ne ta hannun wani saurayinta mai suna Abubakar Usman.
Sauran 'yan tawagar ta'addar da aka kama su na aiki tare da Fatima sun hada da; Sama'ila Usman, mai shekaru 28, Mohammed Ibrahim, mai shekaru 30, Mohammed Agali, mai shekaru 22 da Shamsu Mohammed, mai shekaru 30.
Fatima tare da makaman abokan aikinta Source: Twitter
Sauran sun hada da; Mohammed Usman, mai shekaru 37, Umar Abdullahi, mai shekaru 33, Buhari Abubakar, mai shekaru 33, da Abubakar Garba, mai shekaru 37. An yi kiyasin cewa tawagar 'yan ta'addar sun samu kudi fiye da miliyan goma sha biyu daga aiyukan ta'addanci daban-daban da suka aikata.
Makaman da aka kama tare da 'yan ta'addar sun hada da; bindiga samfurin AK47 guda biyar, babbar bindiga samfurin G3 guda daya, da wata karamar bindiga (Beretta pistol) guda daya. Sauran makaman sun hada da alburusai carbi 1476, carbi 36 na bindigar G3, kwanson aburushin AK47 guda 6, motar hawa guda daya, wayar salula guda 8, da wata akwati mai dauke da kayan aiki daban-daban.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Rundunar 'yan sanda ta cafke wata mata da ke safarar makamai ga masu garkuwa da mutane "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?