
Network 5G: Gaskiyar halinda akeciki akan amfani da 5G network Anajeriya: Minista Sheikh Pantami
Saturday, 4 April 2020
Comment
Gwamnatin Tarayyar najeriya ta bayyana cewa ba ta bawa kamfanonin sadarwar lasisin fara amfani da fasahar intanet ta 5G ba a kasar a cewar ministan sadarawa Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami. A cikin sanarwar da ya fitar dauke da saka hannunsa a ranar Asabar ya ce kawo yanzu Najeriya ba ta fara amfani da fasahar 5G ba kuma ofishinsa bai bawa kowane kamfani lasisin fara amfani da 5G a kasar ba.
Ya ce an dai yi gwaji ne domin duba tasirin fasahar ga lafiyar 'yan kasar kafin a kai ga matakin amince wa shi ko akasin haka. Pantami ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya ba za ta dauki mataki ba har sai ta tuntuni kwararru game da fashar ta 5G kana ta ji ra'ayin 'yan kasar.
Isa Pantami ya ce, "Bisa bayan da ke kan teburi na, hukumar National Frequency Management Council (NFMC) wadda ni ne shugabancinta, ba ta bayar da izinin kafa fasahar 5G ba a Najeriya."PRESS STATEMENT— Fed Ministry of Communications & Digital Economy (@FMoCDENigeria) April 4, 2020
NO LICENCE HAS BEEN ISSUED FOR 5G IN NIGERIA@DrIsaPantami #DigitalNigeria #The5G#5GinNigeria #5GCoronavirus #5GinNigeriaBants #FMoCDEStatement pic.twitter.com/Upkj3T4eNO
Ya kara da cewa, "An tsinkayar da ofishina kan wasu bayanai da ke danganta annobar COVID-19 da fasahar 5G a Najeriya. Saboda haka nake so na fayyace cewa har yanzu ba a bayar da lasisin kafa 5G ba a Najeriya." Wannan na zuwa ne a lokacin da wasu mutane da dama a sassan duniya ke zargin cewa akwai bullar annobar coronavirus yana da alaka da fasahar ta 5G,
wadda hakan yasa suka fara lalata turaken layin intanet har da cinna masa wuta a wasu wuraren. Suma 'yan Najeriya ba a bar su a baya ba a batun inda mutane ke ta bayyana mabanbantan ra'ayinsu game da batun musamman ma a dandalin sada zumunta na Twitter inda ake tattauna batun da maudu'in #5GinNigeria. Daga karshe Pantami ya ce ya umurci hukumar NCC ta amsa tambayoyin 'yan Najeriya game da sabuwar fasahar ta 5G.
LATSA NAN๐๐๐ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐๐๐https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D
0 Response to "Network 5G: Gaskiyar halinda akeciki akan amfani da 5G network Anajeriya: Minista Sheikh Pantami"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?