--
Mutumin da ake zargi da damfara ne ya mallaki kamfanin da ke biza a Najeriya

Mutumin da ake zargi da damfara ne ya mallaki kamfanin da ke biza a Najeriya

Binciken da BBC tare da hadin gwiwar jaridar Premium Times suka gudanar ya gano cewa mutumin da ya mallaki kamfanin da gwamnatin Najeriya ta baiwa kwangilar samar da biza ga mutanen da ke son shiga kasar daga sassan duniya daban-daban yana fuskantar tuhuma kan zargin zamba da halasta kudin haramun a wani kamfanin na daban.

Babu wata alama da ke nuna cewa kamfanin da ke samar da bizar ya aikata ba daidai ba kuma wadannan zarge-zarge ba su da alaka da batun samar da bizar.

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta tuhumi Mahmood Ahmadu, tare da tsohon kamfaninsa Drexel Tech laifukan zamba cikin aminci biyu da kuma na halasta kudin haramun uku.

Mutum uku, ciki har da tsohon ministan cikin gidan kasar Abba Moro, na fuskantar tuhuma kan zamba cikin aminci da keta dokokin bayar da kwangila.

Dukkan mutanen da ake tuhuma, wadanda suka hada da Mr Moro da Mr Ahmadu, sun musanta zargin.

A shekarar 2014, Shugaba Goodluck Jonathan ya karrama Alhaji Ahmadu da lambar girma ta Order Of The Niger, duk da tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Lauyoyinsa sun ce babu wani lokaci da EFCC ko kuma duk wata hukuma a Najeriya ko a wata kasar da ta ayyana shi a matsayin mutumin da ake nema "ruwa-a-jallo". Sun ce ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba. Ya daga cewa bai akata ba daidai ba kuma lauyoyinsa sun musanta cewa yana fuskantar tuhuma.

Sai dai takardun shigar da kara da EFCC ta yi sun yi zargin cewa Mr Ahmadu da wasu mutane na da hannu wajen gudanar da jarrabawar daukar aiki wadda ta yi sanadin mutuwar 'yan Najeriya da dama.

Tsohon kamfanin Mr Ahmadu, Drexel Tech, Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta bai wa kwangila a 2013 domin daukar ma'aikata 4,000.

Ko da yake daga bisani Hukumar ta ce babu wasu gurabe na daukar aiki. 'Yan Najeriya 676,675 suka yi rijistar neman aiki a hukumar inda kowannesu ya biya N1,000 na yin rijista.

Lokacin da aka sanar da ranar daukar aikin, mutane da dama sun mutu a wurin turmutsutsu a yayin da dubban masu neman aiki suka yi tsinke a babban filin wasa na kasa da ke Abuja inda ma'aikatar cikin gidan ta ware domin yin jarrabawar daukar aikin..

Tsohon shugaban hukumar David Paradang ya shaida wa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa: "Na yi mamakin yadda aka gudanar da tsarin daukar aikin domin kuwa ban san za a yi ba."

EFCC ta ce Mr Ahmadu, wanda takardar shigar da kara ta nuna cewa ana nemansa ruwa a jallo, da sauran wadanda ake zargi sun samu kimanin N677m.
                               

Takardar shigar da karar ta kuma yi zargin cewa Mr Ahmadu da kamfanin Drexel Tech Nigeria Ltd sun kashe wani bangare na kudin wajen sayen gidaje a Abuja, yayin da ya ware kimanin N100m, wadanda ya canza zuwa dalar Amurka, domin amfaninsa da kuma kamfaninsa.

Ko da yake dukkan mutanen da ake zargi, ciki har da Mr Moro, sun gabatar da kansu domin yi amsa tambayoyi kuma yanzu haka ana tuhumarsu a kotu, EFCC ta ce Mr Ahmadu bai mika kansa domin a yi masa tambayoyi a kan zargin rawar da ya taka game da daukar aikin ba.

A shekarar 2016, mai magana da yawun EFCC na wancan lokacin, Wilson Uwujiaren ya shaida wa jaridar the Nation cewa: "Za mu iya neman gudunmawar Rundunar 'yan sandan Duniya da sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki a Birtaniya domin su kamo Mahmood Ahmadu. Ya taba mallakar kamfanoni a Birtaniya kuma ta hanyar amfani da bayanansa, ba zai buya ba. Mun riga mun sanya masa ido."


A makon jiya, sabon mai magana da yawun EFCC Tony Orilade ya shaida wa BBC cewa "Mahmood Ahmadu shi ne mai kamfanin Drexel Tech Nig Ltd. Don haka za a iya tuhumarsa.

"Takardar shigar da kara ta nuna cewa ana nemansa ruwa a jallo don haka matsayin hukumar EFCC a bayyane yake: kudaden da aka samu sakamakon hada jarrabawar daukar aikin na haramun ne.... Hukumar EFCC na sane cewa yana boye a Turai. Ba a sake ganinsa ba tun lokacin da aka ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo... kuma tun lokacin da takardar shigar da kara ta ce 'ana nemansa ruwa a jallo'."

Kamfanin yin biza na Mr Ahmadu, Online Integrated Solutions (OIS), ya bayyana ca shafinsa na intanet cewa yana gudanar da ayyukansa a madadin gwamnatin Najeriya a manyan kasashen duniya 25, ciki har da Najeriya China, Lebanon, Hadaddiyar Daular Larabawa, Malaysia, Italiya, Netherlands, Afirka ta Kudu, Amurka, Faransa, Jamus, birtaniya, India da kuma Canada.

Kamfanin yana ikirarin cewa ya yi shura wajen "samar da biza da fasfo a Najeriya" da hadin gwiwar ofisoshin jakadancin da ke fadin duniya domin "bai wa mutane damar yin tafiye-tafiye a duniya ba tare da matsala ba". Kamfanin yana samun ribar miliyoyin fam din Ingila a duk shekara.

BBC ta yi yunkuri da dama domin tuntubar ma'aikatar harkokin gida ta Najeriya da kuma ofishin jakadancin kasar da ke London. Basu ce uffan ba.

Kazalika BBC ta tuntubi Ofishin harkokin kasashen waje da ma'aikatar wajen Birtaniya amma basu shirya yin magana a kan batun ba.


Ma'aikatar Kasuwanci da Makamashi da Masana'antu ta Birtaniya ta ce "dan kasashen waje da ke zaune a Birtaniya amma ake zarginsa da aikata laifi a wata kasar yana iya kafa kamfani a kasar nan idan ba a bayar da sammacin kama shi ba."
KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Mutumin da ake zargi da damfara ne ya mallaki kamfanin da ke biza a Najeriya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?