
Mutanen Ibo sun mikawa Buhari kokon bararsu bayan mutuwar Abba Kyari
Monday, 20 April 2020
Comment
A karshen makon da ya gabata ne COVID-19 ta kashe sugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya. Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Youth Council ta yi magana bayan cikawarsa.
Kungiyar ta OYC ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara la’akarin zaben mutumin Ibo a matsayin sabon sugaban ma’aikatan fadarsa bayan rasuwar Abba Kyari.
Wannan kungiya ta Matasan masu kare hakkin mutanen Ibo a Najeriya ta bayyana cewa an yi babban rashi a game da rasuwar hadimin shugaban kasar wanda ya cika a ranar Juma’a.
Ohanaeze Ndigbo Youth Council ta fitar da jawabi ne a ranar Lahadi 19 ga watan Afrilu, 2020. A wannan jawabi, kungiyar ta yi wa Kyari addu’ar Ubangiji ya yafe masa duk kura-kuransa.
Okechukwu Isiguzoro wanda shi ne shugaban OYC ya fitar da wannan jawabi tare da Sakatarensa na kasa watau Okwu Nnabuike. Hakan na zuwa ne kwana biyu da cikawar Malam Kyari.
Bayan gabatar da ta’aziyya da addu’o’i ga mamacin, kungiyar ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna halin girma, ya tabbatarwa Duniya cewa lallai shi Uban kowa ne a Najeriya.
Mista Okechukwu Isiguzoro da Nnabuike su ka ce shugaban kasar zai canzawa mutane ra’ayinsu a kan shi ne ta hanyar zakulo wanda zai maye wannan gurbi mai tsoka daga Yankin Kudu.
Wannan kungiya ta bukaci sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya fito daga cikin magoya bayansa na mutanen Ibo da ke Kudu maso Gabashin kasar ko bangaren Neja-Delta.
OYC ta ce akwai wadanda su ke tare da shugaban kasar tun lokacin da ya shiga siyasa a 2003 zuwa yau. Kungiyar ta ce Buhari ya na ma iya dauko hadiminsa har daga cikin ‘yan adawa.
“Wannan ce babbar damar da shugaba Buhari ya ke da ita na warkar da Najeriya daga cutar wargajewa da tarwatsewa. Kai, Ibo ne ya shirya yadda jam’iyyu su ka narke a tafiyar APC.”
A ganin matasan na Ohanaeze, idan har shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemo hadiminsa daga yankin Ibo, to ya nuna bajintarsa a siyasa, kuma zai goge kallon da wasu ke yi masa.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Mutanen Ibo sun mikawa Buhari kokon bararsu bayan mutuwar Abba Kyari"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?