
Mutane 23 sun kamu da cutar Coronavirus a jahar Kano, adadinsu ya kai 59
Tuesday, 21 April 2020
Comment
Cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce an samu karin mutane 38 da suka kamu da cutar a Najeriya gaba daya, sai dai a wannan karo ba’a samu ko mutum daya ba a jahar Legas. Sanarwar ta kara da cewa jahar Kano ce kan gaba a jiya inda take da sabbin masu cutar su 23, Gombe na da 5, Kaduna uku, Borno 2, Abia 2, yayin da Abuja, Sokoto da Ekiti suke da 1 kowanne.
“Zuwa karfe 11:10 na daren Litinin, 20 ga watan Afrilu akwai mutane 665 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, inda mutane 22 suka mutu sai 188 da suka warke kuma aka sallamesu.” Inji shi.
Mutane 23 sun kamu da cutar Coronavirus a jahar Kano, adadinsu ya kai 59 Source: Facebook
A hannu guda kuma gwamnatin jahar Sakkwato ta sanar da bullar mugunyar cutar Coronavirus a jahar. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya bayyana haka da kansa cikin wani jawabi da ya yi ma al’ummar jahar Sakkwato inda ya fara da fadin “Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un” Ya cigaba da jawabin sa kamar haka: “Jama’an jahar Sakkwato,
tare da alhini da damuwa nake sanar da ku cewa annobar COVID-19, ma’an Coronavirus ta shigo jahar Sakkwato. A yanzu haka mun fara shirin killace mutumin a wurin killacewa dake Amanawa.” Gwamnan ya ce a yanzu haka mutumin dake dauke da cutar ya fara samun kulawa a asibitin koyarwa ta jami’ar Usmanu Danfodiio dake jahar Sakkwato.
“Ina kira ga jama’a su cigaba da bin ka’idojin da aka shimfida don kare yaduwar cutar nan, muna jin sa ne a baya, amma a yanzu ya shigo cikinmu, don haka ya kamata mu zage damtse domin kare yaduwarsa.” Inji shi.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Mutane 23 sun kamu da cutar Coronavirus a jahar Kano, adadinsu ya kai 59 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?