
Mutane 2 sun mutu a Katsina sanadiyyar harin yan bindiga dadi
Monday, 13 April 2020
Comment
A ranar Juma’a ma yan bindiga sun bude ma wata mota wuta a kan hanyar Faskari daga Sabon Layi makare da Fasinjoji da kaya, inda suka kashe karamin yaro, suka jikkata uwarsa. Shaidu sun bayyana a kullum ana kai ma jama’a hari tare da musu fashi, musamman ma satar babura, wanda ya zama ruwan dare, kuma miyagun suna fakewa ne a cikin dazuka.
Mutane 2 sun mutu a Katsina sanadiyyar harin yan bindiga dadi Source: UGC A hannu guda, mutane 7 sun mutu da yammacin Lahadi, 12 ga watan Afrilu yayin da yan Boko Haram suka kai harin kwantan bauna a kan wasu motocin haya guda 2 a jahar Borno. Boko Haram ta tare motocin ne a wajen garin Auno, kimanin kilomita 20 daga garin Maiduguri, a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu. A kwanakin baya ne gwamnatin jahar Borno ta sanya dokar takaita zirga zirga a kan hanyoyin shiga da fita jahar don kare yaduwar Coronavirus, illa babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Sai dai a yanzu, kwamitin ko-ta-kwana a kan COVID-19 dake karkashin Umar Kadafur ta sanar da garkame hanyar ita ma, kuma dokar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin. Wani matafiyi da ya yi ido hudu da gawarwakin ya bayyana cewa ya kirga gawarwaki guda 7 a wajen garin Auno, kuma an fada musu a daren jiya aka kai harin.
KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Mutane 2 sun mutu a Katsina sanadiyyar harin yan bindiga dadi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?