
Murnar mutuwar Kyari: Kwamishinan da Ganduje ya tube ya yi magana a karo na farko
Sunday, 19 April 2020
Comment
Kwamishinan aiyuka na jihar Kano, Mu'azu Magaji, da gwamna Ganduje ya tube ya yi magana a karon farko tun bayan sanar da sauke shi daga mukaminsa a ranar Asabar. Gwamna Ganduje ya tube kwamishinan ne bisa wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, wato 'facebook', a kan mutuwar Abba Kyari. Jama'a da dama sun fassara rubutun Magaji a matsayin nuna murna da mutuwar Kyari,
lamarin da ya sa har gwamna Ganduje ya sallame shi jim kadan bayan wallafa rubutun. Sai dai, a jawabin da tsohon kwamishinan ya fitar ranar Lahadi, ya ce an yi wa rubutunsa mummunar fassara tare da bayyana cewar shi ba murnar mutuwar Kyari ya ke yi ba. A cikin jawabin, Magaji ya bayyana cewa babu yadda za a yi a matsayinsa na Musulmi ya yi murnar mutuwar wani mutum.
"Na wallafa sakonnin ta'aziyyar marigayi Kyari a shafina na 'facebook' amma babu wanda ya yi wanda ya yi magana, balle a yaba min.
Gwamna Ganduje Source: Twitter
"Wasu mutane ne su ka dauki wani sashe na rubutuna su ka bashi wata fassara ta daban tare da nuna cewa ina kokarin zubar da mutuncin gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da jam'iyyar APC," a cewarsa. A ranar Asabar ne gwamna Ganduje na jihar Kano ya sallami kwamishinan ayyuka da gine-gine na jihar, Injiya Mu'azu Magaji.
Hakan ya biyo bayan mummunan furucin da yayi bayan mutuwar marigayi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari. Mai bada shawara na musamman ga Gwamna Ganduje ne ya wallafa hakan a shafinsa na Tuwita. Legit.ng ta wallafa cewa, kwamishinan Ayyuka da Gine–Gine na jihar Kano, Mu'azu Magaji, ya yi martani a kan rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari inda ya ce yanzu Najeriya ta samu 'yanci. An rantsar da Magaji a matsayin kwamishina ne a ranar 5 ga watan Nuwamban 2O19.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Murnar mutuwar Kyari: Kwamishinan da Ganduje ya tube ya yi magana a karo na farko "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?