
Mun mayarwa direban da dan sanda ya kwacewa N40,000 kudinsa - Hukuma
Monday, 13 April 2020
Comment
- An damke dan sandan da ya aikata wannan abin kunyan Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta mayarwa direban da daya daga cikin jami'anta ya kwacewa kudi N40,000 dan ya hau titi lokacin dokar hana fita a jihar Legas. Kaakin hukumar yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya bayyana hakan ranar Lahadi a wani jawabi inda ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya mayar masa da kudin.
Mun mayarwa direban da dan sanda ya kwacewa N40,000 kudinsa - Hukuma Source: Facebook
Mun kawo muku rahoton wani dan sanda da ke aiki a Okota da ke Oshodi, karamar hukumar Isolo da ke jihar Legas ya shiga hannun hukuma bayan an gano ya karba cin hanci daga masu ababen hawa.
An ga wani dan sanda mai matsayin sifeta mai suna Taloju Martins yana kirga takardun dubu daddaya har guda arba'in a wani bidiyo. Kudin dai tamkar na fansa ne wanda wani mai abun hawa ya bashi don ya sakar masa abun hawansa. Ya zargin mai abun hawan da karya dokar kullen da gwamnatin jihar ta saka don hana yaduwar muguwar cutar coronavirus a jihar ta Legas.
Dan sandan ya bukaci mai abun hawan da aka kwacewa mota da ya biya N50,000 amma sai ya roka aka bar mishi a N40,000. Amma kuma a rashin sanin Martins, mai motar ya nadi bidiyonsa a yayin da suke yin wannan cinikin. Kamar yadda bidiyon da mawaki mai suna Rugged Baba ya wallafa, ya ce lamarin ya faru a ranar Juma'a ne, 10 ga watan Afirilu a titin fadar Ago da ke Okota.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Mun mayarwa direban da dan sanda ya kwacewa N40,000 kudinsa - Hukuma "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?