--
Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade

Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade

- Uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai ta yi zazzafan martani ga danta a twitter - Bello El-Rufai ya yi barazanar fyade ga mahaiifiyar wani wanda sabanin siyasa ya hada su a twitter din

- Jama'a sun fara caccakar uwargidan gwamnan bayan ta ce komai daidai ne soyayya da yaki Uwargidan gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai ta yi martani mai zafi ga danta a kan barazanar da yayi wa wani a twitter. Matar gwamnan, wacce da farko aka fara caccaka a kan kare danta da tayi a ranar Lahadi,

ta bada hakurin cewa sai daga baya ta karanta wallafar danta da kyau. Daga nan ne ta zauna tare da tattaunawa da shi, sannan ta fahimci abinda ke faruwa. Ta ce ba za ta goyi bayan cin zarafi ba kowanne iri kuwa. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin da muhawarar siyasa ta fara ne Bello El-Rufai ya bayyana gazawar shugaban kasar Amurka a yakar annobar Coronavirus. Lamarin ya koma fada tsakaninsa da wani ma'abocin amfani da twitter din.

Abokin fadan ya ce Trump ya fi shugaban kasa Muhammadu Buhari kokari da kuma mahaifin Bello, Gwamna Nasir El-Rufai. Bello ya mayar da martani inda yake cewa: "Ka sanar da mahaifiyarka zan mika ta ga abokaina da daren nan". Masu amfani da kafar sada zumuntar sun fara jawo hankalin matar gwamnan ga wallafar da danta yayi. Ta ce: "Duk masu magana a kan Bello El-Rufai, su daina ambatona. Abinda ka shuka, shi za ka girbe. Komai daidai ne a soyayya da yaki. Ka mutunta kowa amma kada ka amince a taka ka. Ban ga wata barazanar fyade ba."

Amma daga bisani sai uwargidan gwamnan ta wallafa: "A lokacin da nayi wannan rubutun, a zatona fadan da aka saba yi ne a twitter. Na tattauna da Bello. Kada ya sake amfani da barazanar fyade a matsayin makamin yaki" Ta kara da cewa, "Na ga yadda wallafata ta yadu kuma ina bada hakuri ga wadanda ransu ya baci. Ina kara jaddada cewa, ba zan goyi bayan cin zarafi ba kowanne iri kuwa".


KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Matar El-Rufa'i ta caccaki danta da yayi barazanar fyade "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?