
Malaman Jami’a sun zargi Gwamnatin Tarayya da yi masu mugun horo da yunwa
Monday, 20 April 2020
Comment
A daidai lokacin da jama’a su ke jimamin halin da annobar COVID-19 ta jefa Najeriya da wasu kasashen Duniya, kungiyar malaman jami’a ta na nuna cewa abin ya hadu ya yi mata yawa. Kungiyar ASUU ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na horarsu da yunwa a lokacin nan da ake ciki na annoba. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Lahadi, 19 ga watan Afrilu.
ASUU ta ce da ace gwamnatin Najeriya ta yi irin hobbasan da ta ke yi yanzu a harkar lafiya wajen ceto sha’anin ilmi, da yanzu an ga karshen yajin aikin da ake ta fama da shi a jami’o’in kasar. Shugaban wannan kungiya ta ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce idan da gwamnati za ta maida hankali a kan ilmi kamar yadda ake yakar annobar COVID-19, da sai an ga banbanci. Farfesa Biodun Ogunyemi ya ke cewa yajin aikin ASUU ba zai zarce lokacin wannan annoba idan da gwamnati ta yi da gaske. Tun a karshen watan Maris, ASUU ta tafi yajin sai-baba-ta-gani.
Babban Ministan harkar ilmin Najeriya Mallam Adamu Adamu Source: Facebook Biodun Ogunyemi ya ke fadawa ‘yan jarida cewa: “Gwamnati ta jagwalgwala lamarin. A cikin watanni biyun nan, ba a biya ‘ya ‘yanmu da ke jami’o’in gwamnatin tarayya albashi ba.” Da ake hirar da shugaban na ASUU na kasa baki daya, ya nuna zai yi wahala su dawo bakin aiki: “Kun hana mutane albashinsu, kuma ku na tunanin za su koma bakin aiki hankali kwance.”
“A lokacin da ake bada tallafi ga mutane, ka na hana dubban mutane hanyar samun abincincu, kuma ka na tunanin ka na shawo kan matsala ne, ka kulla yaki ne da Malamai masu ilmi.” “Saboda haka kamar wannan gwamnati ta shirya yaki ne da ASUU da ‘ya ‘yanta. Babu wanda ya damu da walwalar iyalin wadanda aka jefa cikin wani hali a sakamakon zaman kulle.” “Mutane sun shiga halin ha’ula’i, ba su da wurin zuwa, kuma ka na amfani da yunwa domin ka azabtar da su, wannan kisan kare dangi ne.” ASUU ta ce akwai bukatar a waiwayi ilmi.
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Malaman Jami’a sun zargi Gwamnatin Tarayya da yi masu mugun horo da yunwa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?