
Mahaifiyar Ado Gwanja da sauran fitattun mutane 15 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 a Kano
Sunday, 26 April 2020
Comment
Jama'ar Kano na zaune cikin fargaba saboda yawaitar mace - macen mutane, yawancinsu tsoffi, da ake samau a cikin birnin jihar. Tun a makon jiya gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya saka dokar kulle jihar Kano; ba shiga, ba fita,
sannan jama'a ma ba za su fito daga gidajensu ba. Gwamnatin jihar ta dauki wannan tsatsauran mataki ne biyo bayan bullar annobar covid-19 a jihar. Duk da gwamnatin Kano ta musanta labarin yawaitar mutuwar mutane a cikin birnin jihar, rahotanni sun bayyana cewa adadin mutanen da ke mutuwa ya na cigaba da aruwa.
An samu mutuwar mutane da dama a cikin birnin Kano da kewaye daga ranar Juma'a zuwa Asabar. Fitattu daga cikin wadanda su ka mutu akwai:
tsohon kwamishina a jihar Kano; Farfesa Ibrahim Ayagi, editan jaridar Triump;
Musa Ahmad Tijjani, tsohon shugaban hukumar ma'aikatan jihar Kano;
Adamu Dal
Sauran sune: Nasiru Maikano Bichi,
Musa Umar Gwarzo,
Ustaz Dahiru Rabi'u, tsohon alkali;
Khadi Salisu Lado,
Nene Umma,
Garba Sarki Fagge,
Salisu Lado,
Shamsiyya Mustapha,
Nene Umma,
Garba Sarki Fagge,
Rabiu Dambatta,
Kabiru Ibrahim Bayero
da mahaifiyar fitaccen mawaki, Ado Gwanja. Gwanja da kansa ya sanar da mutuwar mahaifiyarsa a shafinsa na dandalin sada zumunta, wato 'facebook', inda masoyansa su ka taya shi jaje tare da aika sakon ta'aziyyarsu
Legit.nt ta wallafa rahoton labarin mutuwar Fitaccen masanin ilimin tattalin arziki, Farfesa Ibrahim Ayagi, wanda ya mutu ranar Asabar a jihar Kano. An haifi marigayi Ayagi a shekarar 1940 a jihar Kano, ya mutu yana da shekara 80 a duniya bayan ya sha fama da rashin lafiya.
An yi jana'izarsa bayan sallar La'asar a gidansa da ke kallon makarantar sakandiren Gwale a cikin garin Kano. Marigayi Ayagi, wanda ake girmamawa saboda iliminsa a bangaren tattalin arziki, ya taba rike babban darektan bankin 'Continental Merchant Bank'. Farfesa Ayagi ya taba rike kujerar kwamishinan cigaban tattalin arzikin jihar Kano daga shekarar 1975 zuwa 1978. Kazalika, ya rike mukamin babban darektan gidauniyar jihar Kano (Kano Foundation) daga shekarar 1987 zuwa 1990.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Mahaifiyar Ado Gwanja da sauran fitattun mutane 15 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 a Kano "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?