--
Mahaifin akanta janar na Najeriya ya mutu a Kano

Mahaifin akanta janar na Najeriya ya mutu a Kano



Mahaifin Ahmed Idris, babban akanta na kasa, ya mutu ranar Laraba a jihar Kano, kamar yadda sanarwa ta nuna.

Sanarwar mutuwar na kunshe ne a cikin wani sako da Henshaw Ogubike, kakakin babban akanta na kasa, ya aika wa manema labarai ranar Laraba.

"Mu na ma su bakin cikin sanar da mutuwar Alhaji Idris Hussain, mahaifin Ahmed Idris, FCNA, babban akanta na kasa. Ya koma ga mahaliccinsa ranar Laraba da safe. Ya mutu ya na da shekaru 96 a duniya.

"Dattijon ya mutu ne bayan ya sha fama da jinya.

"Marigayi Ahaji Idris Hussain dan kasuwa ne mai son taimakon ma su karamin karfi da marayu. Ya yi rayuwarsa a unguwar Daneji da ke karkashin karamar hukumar birnin Kano a jihar Kano.

"Ya mutu ya bar 'ya'ya da jikoki da tattaba kunne ma su yawa. Daga cikin 'ya'yansa akwai Alhaji Ahmed Idris, FCNA, babban akanta na kasa.

"An binne shi bisa tsarin addinin Musulunci a Kano.

"Mu na sanar da jama'a cewa ba za a yi zaman makoki ba saboda dokar nesanta da zama a gida da gwamnatin tarayya ta saka domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

"Ga ma su son kai ziyarar ta'aziyya, za su iya aika sakon waya ko kuma su aika sakonsu ta dandalin sada zumunta. Allah ya ji kansa," a cewar sanarwar.

A ranar Talata ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin bincike don gano sanadiyyar yawan mace-macen mutane da ake samu a Kano a 'yan kwanakin baya bayan nan.

A kalla mutum 40 ne aka birne tun bayan bullar muguwar cutar coronavirus a makabartar Dandolo da ke karamar hukumar Dala ta jihar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ana samun mamata a kalla uku zuwa biyar ne a kowacce rana.

A makabartar kofar Mazugal kuwa, ana birne a kalla mutum 10 yanzu a kowacce rana, lamarin da ya tada hankulan jama'a sannan suka bukaci a bincika dalili.

Kazalika, a makabartar Kara da ke kusa da mayanka, Aminu Koki ya sanar da jaridar The Nation cewa an birne gawawwaki 42 tsakanin ranar Litinin zuwa Talata.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Related Posts

0 Response to "Mahaifin akanta janar na Najeriya ya mutu a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?