--
Ku lallaba mazajenku kada ku tsokana rigimar da tafi ta Coronavirus - Budurwa ta shawarci matan aure

Ku lallaba mazajenku kada ku tsokana rigimar da tafi ta Coronavirus - Budurwa ta shawarci matan aure

- Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ta shawarci mata a kan zama da mazansu a wannan lokacin hutun dolen

- Ta ce ba ta goyon bayan namiji ya daga hannu ya daki mace amma wasu matan halayyarsu ce ke ja musu - Kalubalantar namiji kuwa babbar matsala ce don babu namijin da ke son kalubale balle daga matar shi Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ta shawarci mata da su kiyaye kalamansu da sauran lamurransu a yayin da maza ke kulle a gida sakamakon annobar coronavirus.

A cewarta, hakan ne kadai zai tseratar da mata daga shan duka a wurin mazansu. Budurwar mai sun Mma Eka ta bayyana cewa bata goyon bayan namiji ya daga hannun shi a kan matarshi amma kuma kada matar da ta kai namijin makura. Kowanne namiji yana da iya abinda zai iya jurewa amma zai iya barna idan aka kure shi.

Ku lallaba mazajenku kada ku tsokana rigimar da tafi ta Coronavirus - Budurwa ta shawarci matan aure Source: Facebook "

Bana goyon bayan namiji ya daga hannu a kan matar shi komai kuwa laifin da tayi mishi a duniya. Amma kuma babu dadi mace ta kai namiji makura don kowanne namiji yana da iyakar hakurin shi.

"Ku daina yi wa maza amfani da kalamai irinsu: Ba za ka iya yin komai a kai ba, me za ka iya yi? Yi duk abinda za ka iya... Wadannan kalaman na kalubale ne kuma babu namijin da zai iya jure ana kalubalantar shi. A dena amfani da baki kamar lalataccen famfo." Ta ce.

Ta kara da bayyana yadda wasu matan ke kaiwa ga shake wuyan rigar namiji ko dukan kirjin shi tare da ihun cewa ko zai kashesu ba za su daina abinda suke yi ba. "Kada ki bata mijinki da kanki don daga baya ke za ki yi dana-sani. Kun ga wannan hutun dole da suke yi a gida, kada ki yi ganganci idan baki son ganin aikin ganganci. A jiya na shawarci maza a kan yadda za su zauna lafiya da matansu a wannan lokacin, yanzu lokacin ki ne."

Ta kara da cewa. Kamar yadda tace, an san mata da kaifin harshe amma mace mai hankali ta san lokacin da za ta yi magana. Akwai karin magana mai cewa "Za ka iya dana-sani a kan kalamanka amma ba za ka iya taba dana-sanin shirunka ba."
LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ku lallaba mazajenku kada ku tsokana rigimar da tafi ta Coronavirus - Budurwa ta shawarci matan aure "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?