--
Ko masu cin kare a Nigeria za su iya hakura lokacin coronavirus?

Ko masu cin kare a Nigeria za su iya hakura lokacin coronavirus?

Annobar coronavirus wadda ta addabi duniya ta sanya hukumomi sake nazari kan wasu nau'o'in abincin da mutane ke ci wadanda suke jin na da illa ga lafiyar al'umma.
Kwararru dai na alakanta asalin cutar coronavirus da cin namun daji ciki har da kare da mage.
Shenzhen ya zama birni na farko da ya haramta sayarwa da cin naman kare da na mage a kasar China don hana yada bakin cutuka irinsu Coronavirus.
Matakin na zuwa ne bayan barkewar annobar koronabairas wadda ake alakantawa da naman dabbobin daji, abin da ya ingiza hukumomin China haramta cinikayya da cin dabbobin daji.
Sabuwar dokar haramta cin naman kare da na mage za ta fara aiki ne a birnin Shenzhen din daga ranar 1 ga watan gobe.

Kwararru a fannin ilmin kimiyya da masu bincike har yanzu ba su kai ko kusa ga gano tushen inda kwayar cutar koronabairas ta fito da ma yadda ta yadu zuwa ga dan'adam.
A Najeriya ma, akwai al'umomin da naman kare da na mage, wani muhimmin kayan dadi ne a gargajiyance da har yanzu suke alfahari da shi.
BBC ta yi tattaki zuwa Mabushi - daya daga cikin unguwannin da ake samun masu sayarwa da cin naman kare a Abuja, babban birnin kasar.
Wani bangare na unguwar dai na dauke da al'ummomi masu karamin karfi kuma suna rayuwarsu ciki har da hada-hadar saye da sayar da naman kare.
Wani mazaunin yankin da ke sana'ar sayar da kare (ko da yake bai so a ambaci sunansa ba) ya ce suna sayen kare a kan N8,000 zuwa N10,000 gwargwadon girmansa, haka gwargwadon kudinsa.
"Muna samun ribar N2,000 idan muka sayar da karen da muka saya a kan N10,000 ," a cewarsa.
Ya ce mutane da yawa suna zuwa sayen naman kuma "ana taruwa ne (waje daya) a ci a sha a yi nishadi".
Sai dai ya ce ba su da masaniya cewa cin naman karen yana haddasa cutuka.
"Kare nama ne mai dadi, kuma duk jikinsa babu abin yasarwa, daga kafafuwa, har kai, dabba ce mai lagwada", in ji dillalin karnuka.

Ita ma wata mai sana'ar sayar da naman kare da burkutu ta shaida wa BBC cewa tana kiwon karnuka sannan kuma tana saya a hannun masu kiwo, don yankawa ta sayar da nama.
Ta kara da cewa wani lokaci masu karen da suke da sha'awar sayarwa suna tuntubar ta ko za ta sayi karen.
Game da ko suna kai karen asibitin dabbobi a duba lafiyarsa, matar ta bayyana cewa "gaskiya ba ma yin haka, amma muna yanka shi, idan muka ga yana da (koshin) lafiya."
"(Muna) sa wa karen zarge a makure shi kuma idan (jikinsa) ya yi sanyi, sai a yanka saboda idan an kama shi haka zai iya cizo."
Ta bayyana cewa za ta ci gaba da sayarwa da kuma cin naman karen sai dai fa idan an tabbatar da mata da hatsarin cin naman karen da kuma alakarsa da cutuka irinsu coronavirus.





A sassan yankin nahiyar Asia, ana yanka kare miliyan 30 duk shekara, kamar yadda kungiyar Humane Society International (HSI) ta bayyana.
Kazalika, hukumomi a Koriya ta Kudu sun fara rushe mayankar karnuka mafi girma a kasar.
Za kuma a mayar da mayankar zuwa wajen shakatawar jama'a.
Kimanin kare miliyan daya ake ci kowace shekara sai dai masu rajin kare dabbobi na neman a kawo karshen wannan al'ada.
KARANTA: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

DAGA MUJALLAR:https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ko masu cin kare a Nigeria za su iya hakura lokacin coronavirus?"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?