
Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19
Friday, 24 April 2020
Comment
Tun bayan bullar cutar Covid19 a birin Wuhan da ke kasar China a karshen shekarar 2O19, cutar ta cigaba da bazuwa a duniya kamar wutan dare inda ta ke ta kashe mutane da dama. Hakan ya faru ne saboda rashin takamammen magani ko rigafi na kwayar cutar duba da cewa sabuwar cuta ce da ba taba ganin ta a duniya ba. Ana ta gwaje gwajen magunguna da dama a kasashen duniya daban daban amma kawo yanzu ba a cimma gano takamemen magani ko rigakafi da hukumar lafiya ta duniya ta amince da ingancin shi ba.
Bullar cutar ya kawo sauye sauye a yadda kasashe ke gudanar da harkokin baki daya inda mafi yawanci kasashe suka rufe iyakokin su tare da saka dokar kulle a birane da dama ciki har da Najeriya. Duk da cewa cutar ta kashe mutane da dama, akwai wasu mutanen da suka kamu amma daga bisani suka warke da taimakon likitoci.
Ga dai kiddigan kasashe 1O da cutar ta kama mutane tare da adadin wanda suka warke da kuma wadanda suka riga mu gidan gaskiya zuwa ranar 23 ga watan Afrilu kamar yaddda Tracking meters ta wallafa. 1. Amurka Wandanda suka kamu - 849,092 Wadanda suka mutu - 47,681 Wadanda suka warke - 84,050 2. Spain Wandanda suka kamu - 208,389 Wadanda suka mutu - 21,717 Wadanda suka warke - 85,915 3. Italy Wandanda suka kamu - 187,327 Wadanda suka mutu - 25,085 Wadanda suka warke - 54,543 4. Faransa Wandanda suka kamu - 159,877 Wadanda suka mutu - 21,340 Wadanda suka warke - 40,657
5. Jamus Wandanda suka kamu - 150,648 Wadanda suka mutu - 5,315 Wadanda suka warke - 103,300 6. Burtaniya Wandanda suka kamu - 133,495 Wadanda suka mutu - 18,100 Wadanda suka warke - Ba a san adadin ba 7. Turkiyya Wandanda suka kamu - 98, 674 Wadanda suka mutu - 2,376 Wadanda suka warke - 16,477 8. Iran Wandanda suka kamu - 85,996 Wadanda suka mutu - 5,391 Wadanda suka warke - 63,113 9. China Wandanda suka kamu - 82,798 Wadanda suka mutu - 4,632 Wadanda suka warke - 77,207 10. Rasha Wandanda suka kamu - 57,999 Wadanda suka mutu - 513 Wadanda suka warke - 4,420
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Kasashe 10 da aka fi samun masu dauke da cutar COVID-19 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?