
Karya dokar ta-baci yasa za’a iya samun mutane 57,000 da zasu kamu da Corona a Kaduna
Monday, 13 April 2020
Comment
Gwamnatin ta damu ne bayan samun mutum na 6 dake dauke da cutar, wanda ya dawo daga jahar Legas, kuma motar haya ya bi, bayan an tabbatar da cutar a jikinsa ta hanyar gwaji. Daga nan ne gwamnatin jahar ta fara dabbaka dokar da karfin tuwo domin tabbatar da jama’a sun zauna a gidajensu, tare da hana tafiye tafiye, har sai baba ta ji, domin hana yaduwar cutar.
Jama'an Kaduna Source: Twitter
Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka inda ya jaddada bukatar jama’a su daina fita don kare kansu. Aruwan yace sun umarci jami’an tsaro su mayar da duk wani matafiyi dake kokarin bi ta garin Kaduna, sai dai idan sun samu izinin ratsa garin ko kuma suna dauke da muhimman abubuwa.
Rahoton ta kara da cewa an kama motoci da dama a hanyar Kachia da Sabon Tasha, yayin da wasu direbobin suka saki motocinsu suka tsere don gudun kamen jami’an tsaro. A wani labarin, Hukumar NCDC ta sanar da samun mutane 5 da suka kamu da annobar Coronavirus a Najeriya, wanda ya kawo adadin masu dauke da cutar zuwa 323.
Zuwa karfe 9:10 na daren Lahadi, akwai mutane 323 da aka tabbatar suna dauke da cutar COVID-19 da aka samu rahotonsu a Najeriya, 10 sun mutu, yayin da an sallami 85. Jahohin da aka samu sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun hada da jahar Legas, mutane biyu, jahar Kwara ita ma da mutane biyu sai kuma jahar Katsina inda mutum daya ya kamu.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657 c
0 Response to "Karya dokar ta-baci yasa za’a iya samun mutane 57,000 da zasu kamu da Corona a Kaduna "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?