
Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)
Saturday, 25 April 2020
Comment
- A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da sassauta dokar hana zirga-zirga ta jihar don jama'a su yi siyayyar azumin watan Ramadan - An ga kasuwanni sun yi matukar cika da jama'a inda suke ta hada-hadar siyan abubuwan bukata na amfanin gida
- Amma kuma wani hanzari, farashin kayayyakin bukata ya yi matukar tashi duk da cewa 'yan kasuwar na ajiye da kayan ne ba yanzu suka saro su ba Kasuwannin jihar Kano sun yi matukar cika a ranar Alhamis bayan gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana zirga-zirga da ta kafa a jihar don jama'a su shiryawa azumin watan Ramadan. A kasuwar Tarauni inda ake siyar da kayan miya da sauran abubuwa masu lalacewa, an ga jama'a masu tarin yawa suna siyayyar kayan bukata.
Hakazalika, a kasuwar Dawanau wacce ita ce cibiyar kasuwancin hatsi a Afrika ta yamma, an ga dandazon jama'a na siye da siyar da hatsin don Ramadan da kuma kullen sati biyu da za su fuskanta.
Kamar yadda wani dan kasuwa, Alhaji Danliti Adam yace, an samu kari a farashin kayayyakin abinci a kasuwar tun bayan saka dokar. Ya ce, duk da sun shirya wa irin wannan al'amarin, amma 'yan kasuwa basu da kayan siyarwa a kasa yanzu.
A kasuwar Yankura da ke Yankaba inda ake siyar da kayayyakin lambu, jaridar Daily Trust ta lura cewa an samu tarin mutane ba kamar yadda aka saba ba. Aminu Ibrahim Yankaba ya ce ya matukar yin mamakin yadda 'yan kasuwa suka hanzarta tada farashin kayayyaki. Alhaji Muhammad Inuwa ya sanar da jaridar Daily Trust cewa ba shi da zabin da ya wuce ya siya kayayyakin da yake bukata duk da karuwar farashin.
Ya ce, "Idan ban siya ba yanzu, yaushe nake da tabbacin gwamnatin za ta sassauta dokar? Zai fi kyau in siya abinda zan iya siya yanzu tunda ina bukata. "Ina da tabbacin cewa babu wanda yake farin cikin halin da muka samu kanmu, amma babu abinda za a iya a kai. Zai fi kyau idan muka sauya tsarin rayuwarmu."
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Kano: Dandazon jama'a na siyen kayan amfani bayan sassauta doka (Hotuna)"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?