
Kaico! Jirgin yakin Najeriya ya yi ma kananan yara luguden wuta a jahar Borno
Monday, 13 April 2020
Comment
Akalla mutane 17 ne suka mutu yayin da jirgin yakin Najeriya ya jefa bamabamai a kauyen Sakotoku dake karamar hukumar Dambo ta jahar Borno, bisa kuskure. Jaridar TheCable ta ruwaito wadanda suka mutu a wannan harin sune mata da kuma kananan yara, wanda suke wasa da zaman shan iska a karkashin wata bishiyar mangwaro.
“Bamu sani ba ko an samu gibi a musayar bayani ne tsakanin Sojojin sama da na kasa a lokacin da jiragen rundunar Sojin sama suka jefa bamabamai a kauyen ba, mutane 17 sun mutu, yawancinsu mata da kananan yara ne dake wasa a kasar bishiyar mangwaro. “Da dama kuma sun samu rauni, kuma an garzaya dasu zuwa asibitin runduna ta 25 dake Damboa, wadanda ke cikin mawuyacin hali kuma an mika su zuwa Maiduguri. Wadanda harin ya shafi gidajensu kuma sun zarce Damboa.” Inji majiyar.
A wani labari kuma, mutane 7 sun mutu a ranar 12 ga watan Afrilu yayin da yan ta’addan Boko Haram suka kai hari kwantan bauna a kan wasu motocin haya guda 2 a jahar Borno. Premium Times ta ruwaito Boko Haram ta tare motocin ne a wajen garin Auno, kimanin kilomita 20 daga garin Maiduguri, a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu. Wani matafiyi da ya yi ido hudu da gawarwakin ya bayyana cewa ya kirga gawarwaki guda 7 a wajen garin Auno, kuma an fada musu a daren jiya aka kai harin.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Kaico! Jirgin yakin Najeriya ya yi ma kananan yara luguden wuta a jahar Borno "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?