
Kaduna: 'Yan sanda sun kama wani matashi da ya yi batanci ga Annabi a dandalin sada zumunta
Tuesday, 28 April 2020
Comment
"An haifi Mubarak a gidan Musulunci amma saboda wasu dalilai na kashin kansa sai ya zabi ya bar addinin, ya zama marar addini, a 2014. Tun da ya bar addini ya ke wallafa sakonnin da basa yi wa Musulmai dadi a shafinsa na 'facebook'. Wata majiya ta ce wasu jami'an 'yan sanda ne guda biyu, a cikin fararen kaya, suka je har gida suka kama Mubarak tare da tafiya da shi ofishinsu mafi kusa da gidan da yake zaune a Kaduna.
Wani mamba a wata kungiya da Mubarak ke zaman shugaba ya shaidawa manema labarai cewa suna bukatar a gaggauta sakinsa ba tare da wani bata lokaci ba. "Mun damu matuka da kama shugabanmu, Mubarak Bala, da aka yi.
"Watakila rundunar 'yan sandan Kaduna za ta mika shi hannun 'yan sanda a Kano, inda ake so a gurfanar da shi a gaban kotu saboda suna aiki da dokar Musulunci ta kashe ma su batanci ga addini. "Mu na rokon babban sifeton rundunar 'yan sanda da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa'i, a kan su saka baki domin a gaggauta sakinsa," a cewarsa.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Kaduna: 'Yan sanda sun kama wani matashi da ya yi batanci ga Annabi a dandalin sada zumunta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?