--
Ka tuba ka ajiye makaman ka ko kuma ka tafi kiyama – Sakon shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ga Shekau

Ka tuba ka ajiye makaman ka ko kuma ka tafi kiyama – Sakon shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ga Shekau

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, yayi kira ga shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, da ya tuba ya ajiye makaman yakinsa ko kuma ya kashe shi.

Wannan dai ya zo ne kwanaki kadan bayan shugaban kasar Chadin ya jagoranci tawagar sojojin kasar sun kaiwa ‘yan ta’addar Boko Haram din hari, inda suka kashe kimanin mutum 100 daga cikinsu.

A wata sanarwa da ya fitar ga al’ummar kasar, shugaban kasar wanda yayi magana cikin harshen Faransanci, ya ce yanzu ne Shekau yake da damar ajiye makaman yakinsa ya fito ya tuba, ko kuma ya mutu duk da cewa yana boye a cikin daji Dikoa, inda ya kara da cewa zai kashe Shekau kamar yadda ya kashe manyan yaransa.

A rahotannin da Daily Trust ta bayar, ‘yan ta’addar sun kai wani harin kwanton bauna ga sojojin kasar Chadin, inda suka kashe kimanin sojoji 92 a lokacin.

Shugaba Deby, wanda ya ce ba zai taba yadda da irin wannan kisan kiyashi da aka yiwa sojojinsa ba, ya dauki runduna da kanshi domin daukar fansar kisan da aka yiwa sojojin nasa.

Rundunar ta kai wannan hari ne a ranar Alhamis, haka kuma ta kara kaiwa ‘yan ta’addar hari a yankin Kelkoua da Magumeri, inda suka tarwatsa sansanin ‘yan Boko Haram din, suka kwace makamai masu yawan gaske sannan suka kama daya daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram din.
KARANTA: Sautin murya: Shekau ya yi laushi a cikin sabon sakon da ya fitar don karfafawa mayakansa gwuiwa

DAGA MUJALLAR:https://www.bzglobalservice.com.ng/

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 





Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Ka tuba ka ajiye makaman ka ko kuma ka tafi kiyama – Sakon shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ga Shekau"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?