--
Jihohi 33 a Najeriya wanda cutar Coronavirus ta bulla - NCDC

Jihohi 33 a Najeriya wanda cutar Coronavirus ta bulla - NCDC



Likafar annobar cutar korona na ci gaba a Najeriya duk da irin kai komo da mahukuntan lafiya ke yi babu dare babu rana domin dakile yaduwar cutar a kasar. A halin yanzu an samu bullar cutar korona a jihohi 33 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda alkaluman cibiyar dakile yaduwar cututtuka a kasar NCDC suka tabbatar. Taskar bayanai ta NCDC a ranar Lahadi 26 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 1273 yayin da tuni mutum 239 suka warke.

Ya zuwa yanzu dai mutane 40 cutar ta hallaka a fadin Najeriya kamar yadda kididdigar alkaluman ta tabbatar. Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 25 na Najeriya da cutar ta bulla:

 Lagos-731; Abuja-141; Kano-77; Ogun-35; Gombe-35; Osun-34; Katsina-30; Borno-30; Edo-25; Oyo-21; Kaduna-15; Bauchi-14; Akwa Ibom-12; Kwara-11; Sokoto-10; Ekiti-8; Ondo-8; Rivers-6; Delta-6; Taraba-6; Jigawa-2; Enugu-2; Niger-2; Abia-2; Zamfara-2; Benue-1; Anambra-1; Adamawa-1; Plateau-1; Imo-1; Bayelsa-1; Ebonyi-1; Kebbi-1.



Da misalin karfe 11.50 na daren ranar Lahadi, cibiyar mai fafutikar dakile yaduwar cututtuka ta sanar da cewa an samu karin mutane 91 da cutar covid-19 ta harba a fadin Najeriya. An samu karin mutum 91 ne daga jihohi 16 na kasar da suka hadar da; Legas (43), Sokoto (8), Taraba (6), Kaduna(5), Gombe (5), Ondo (3), Abuja (3), Edo (3), Oyo (3), Rivers (3), Bauchi (3), Osun (2), Akwa Ibom (1), Bayelsa (1), Ebonyi (1) da kuma Kebbi (1).

Jihohin Najeriya da cutar ta bulla karo na farko a baya-bayan nan sun kasance Ebonyi a yankin Kudu maso Gabas, Bayelsa a yankin Kudancin Kudu, Kebbi a yankin Arewa maso Yamma da kuma Taraba a yankin Arewa ta Tsakiya. Har ila yau dai jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan wadanda cutar ta kama inda adadinsu ya kai 731, sai kuma birnin tarayya inda cutar ta harbi mutum 141 yayin da jihar Kano ta biyo baya da mutum 77.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Jihohi 33 a Najeriya wanda cutar Coronavirus ta bulla - NCDC"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?