
Jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida a Najeriya - NHRC
Thursday, 16 April 2020
Comment
Tare da saka dokar takaita zirga-zirga a sauran sassan kasar domin dakile yaduwar annobar covid-19. A cewar alkaluman hukuma, mutane 407 sun kamu da cutar covid-19 a jihohi fiye da 20. An baza jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da sojoji domin tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga dokar zaman gida da hukuma ta saka. A wani rahoto da NHRC ta fitar ranar Laraba, ta bayyana cewa, "mun samu korafi 105 a kan take hakkin bil'adama da jami'an tsaro su ka yi a jihohi 24.
"Daga cikin korafin, akwai kisan gilla da aka yi wa mutane 8, lamarin da ya kawo jimillar mutanen da aka kashe zuwa 18," a cewar NHRC.
Jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida a Najeriya - NHRC Source: Depositphotos
NHRC ta ce adadin mutanen da jami'an tsaro su ka kashe sun fi yawan wadanda annobar covid-19 ta hallaka. "A yayin da cutar covid-19 ta kashe mutane 11 a fadin kasa, jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida," a cewar rahoton NHRC na ranar Laraba.
Hukumar ta zargi jami'an tsaro da amfani da karfi a kan fararen hula, amfani da iko ta hanyar da bai dace ba, cin hanci, da saba ka'idojin aikin tsaro na Najeriya da kasa da kasa. Sai dai, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Frank Mba, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa,
"NHRC bugu ta ke yi ba kama suna a cikin zarginta. "Ya kamata hukumar NHRC ta fitar da bayanai a kan mutanen da aka kashe, kuma ya kamata ta bayar da cikakken bayani a kan jami'an tsaron wacce hukuma ne su ka kashe mutanen, kuma a ina." Mba ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda za ta cigaba da aikinta na tabbbatar da doka bisa tsarin dokokin aiki da na kasa.
KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Jami'an tsaro sun kashe mutane 18 yayin tabbatar da dokar zaman gida a Najeriya - NHRC "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?