
Iyalan mamaci 5 ko 6 kadai muka amince su yiwa gawa Sallar Jana'iza - Gwamnatin Saudiyya
Wednesday, 15 April 2020
Comment
Ma'aikatar kiwon lafiyan kasa tace mutane biyar zuwa shida daga iyalan mamaci ne aka amince su gudanar da Sallar Jana'iza. Yayinda ministan lamuran addinin Musulunci, Da’awah, da shiryar da a’umma na Saudiyya, Dr. Abdul Latif Al Sheikh, yake tsokaci kan hakan, ya ce Sallar Jana'iza bata na farilla muhimmanci ba. Yace taruwar mutane a waje na iya rura yaduwar cutar cikin al“umma.
Yace “Wannan mataki ne da aka dauka na haramta taro na cewa a yi Sallolin Jana'iza a makabartu kuma kada iyalan mamacin sun wuce biyar ko shiga, sauran suyi sallarsu a gida.“
A nan gida Najeriya, Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce gwamnati ba zata bayar da gawawwakin wadanda suka mutu sakamakon cutar Coronavirus ga iyalansu domin birnesu ba. Ya ce ma'aikatar kiwon lafiya za ta birne saboda ana iya kamuwa da cutar daga cikin mamaci. Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi a taron kamfanin dillancin labarai NAN a Abuja. A cewar NAN,
ministan ya yabawa yan Najeriya bisa biyayyar da suka yiwa gwamnati kan dokar hana fita. Yace: "Coronavirus cuta ce mai matukar hadari; har yanzu ba'a samu maganinta ba kuma ta nada ikon kisa, gajiyar da sashen kiwon lafiya da kuma karya tattalin arziki." "A wasu kasashe cikin firji ake ajiye gawawwaki saboda dakunan ajiye gawawwaki sun cika. Yan Najeriya su sani cewa wannan ba irin gawawwakin da za'a basu bane su birne saboda hakkin ma'aikatar kiwon lafiya ne."KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Iyalan mamaci 5 ko 6 kadai muka amince su yiwa gawa Sallar Jana'iza - Gwamnatin Saudiyya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?