--
Hana fita da taron jama'a: An kama babban Limami, an kwace motoci 269 a Abuja

Hana fita da taron jama'a: An kama babban Limami, an kwace motoci 269 a Abuja

Kwamitin tabbatar da biyayya ga umarnin zama a gida da hana taron jama'a a Abuja ya kama wani shugaban al'ummar Musulmi da ya sabawa matakin da hukuma ta dauka domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19. Shugaban kwamitin, Ikharo Attah, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja ranar Lahadi.

Ya kara da cewa, jami'an kwamitinsa sun kwace motoci 269 bayan samunsu da laifin sabawa umarnin a zauna a gida. "Mun fara aiki da sanyin safiyar yau (Lahadi) bayan wasu 'yan kasa nagari sun kiramu tare da sanar da mu cewa za a yi taron ibada a wata coci da ke unguwar Durumi. "Bayan mun isa Cocin sai muka iske cewa hakan ba gaskiya bane, amma mun sami Fasto a cikin Cocin tare da masu daukan hoton bidiyo. "Daga nan sai muka wuce zuwa wani Masallaci da aka tabbatar mana da cewa babban Limamin Masallacin ya jagoranci jama'a sallar Juma'a a yankin Wuye," a cewar Attah.

A wani labarin mai nasaba da wannan, Legit.ng ta wallafa cewa 'yan sanda a jihar Nasarawa sun kama manyan jami'an gwamnatin jihar da suka karya dokar da gwamnan jihar, Abdullahi Sule, ya kafa a kan killace kai tare da hana taron jama'a saboda dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Manyan jami'an gwamnatin da aka kama sune; Alhaji Suleman Agyo, shugaban karamar hukumar Lafiya ta kudu da Mukhtar Wakeel, mukaddashin rijistara a kwalejin kimiyya da fasaha da ke garin Lafiya. Faifan bidiyon bikin auren shugaban karamar hukumar ya yadu a dandalin sada zumunta, musamman a tsakanin mazauna garin Lafiya. Da ya ke tabbatar da kama manyan jami'an gwamnatin a ranar Lahadi, kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa, Bola Longe, ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhumarsu da laifin sabawa umarnin gwamnatin jiha.KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
                            LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Hana fita da taron jama'a: An kama babban Limami, an kwace motoci 269 a Abuja "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?