
Gwamnoni sun bukaci Buhari ya sassauta dokar hana zirga-zirga
Sunday, 26 April 2020
Comment
Gwamnonin Najeriya sun baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara da ya dan sassauta dokar hana zirga zirga da aka sanya a wasu Jihohi domin dakile yaduwar cutar coronavirus wadda ke shirin karewa yau lahadi.
Gwamnonin sun bukaci shugaban da ya hana zirga zirga tsakanin Jiha zuwa wata Jiha, amma kuma ya bada izinin zirga zirga a cikin Jihohin domin baiwa jama’a damar walwala.
A wata wasika da suka rubutawa Sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha, Gwamnonin sun bukaci hana mutane gudanar da tarurruka da kuma tilasta amfani da kyallen dake rufe fuska.
Wasikar dake dauke da sanya hannun gwamnan Ekiti Kayode Fayemi yace bayan tattaunawa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sun amince su gabatar da bukatun su domin sanyawa cikin ayyukan da kwamitin ko ta kwana na gwamnatin Najeriya ke aiki da shi wajen yaki da cutar coronavirus.
Gwamnonin sun kuma bukaci shugaba Buhari da ya cire masu safarar abinci da kayan marmari da magunguna da kayan asibiti da man fetur da kuma amfanin gona cikin wadanda aka hana zirga zirga.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Gwamnoni sun bukaci Buhari ya sassauta dokar hana zirga-zirga"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?