
Gwamnoni sun amince da dokar kulle duk jihohin Najeriya na tsawon kwanaki 14
Wednesday, 22 April 2020
Comment
A ranar Laraba ne dukkan gwamonin jihohin Najeriya 36 su ka amince da kaddamar da dokar kulle kasa baki daya har na tsawon sati biyu domin dakile yaduwar annobar covid-19. Gwamnonin, a karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF),
sun cimma wannan matsaya ne bayan sauraron bayanai daga gwamnonin jihohin Lagos, Bauchi, Oyo da Ogun a kan darussan da su ka koya daga yaki da annobar covid-19. Shugaban kungiyar NGF, gwamnan jihar Ekiti,
Kayode Fayemi, ne ya fitar da wannan sanarwa bayan kammala taron gwamnonin da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar kiran waya mai nuna bidiyo. A cikin sanarwar, Fayemi ya bayyana cewa babu wanda za a yi wa uzuri sai ma su aiyuka ko bukatu na musamman.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Gwamnoni sun amince da dokar kulle duk jihohin Najeriya na tsawon kwanaki 14 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?