
Gwamnatin tarayya ta fara raba N20,000 ga talakawa a Abuja
Wednesday, 1 April 2020
Comment
Ministar walwala, manajin annoba da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta rabawa mutanen karamar hukumar Kwali dake Abuja da kanta a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, 2020.
"Za'ayi hakan a dukkan jihohin Najeriya, amma mun fara da Abuja, Legas da Ogun. Sune kan gaba (wajen yaki da cutar Coronavirus). Sauran jihohin zasu biyo baya."
"A yau muna bada N20,000 ga mutane 190 a Kwali. Mutane 5000 zasu amfana da wannan kudin a birnin tarayya Abuja."
Hajiya Sadiya ta jaddada da cewa ba'a yi son kai wajen zaben wadanda ake biya ba kuma ba yan wata jam'iyyar siyasa bane.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
b
0 Response to "Gwamnatin tarayya ta fara raba N20,000 ga talakawa a Abuja"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?