--
Gwamna Badaru ya kulle karamar hukumar Kazaure bayan bullar annobar covid-19

Gwamna Badaru ya kulle karamar hukumar Kazaure bayan bullar annobar covid-19

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanare da kulle karamar hukumar Kazaure bayan tabbatar da samun bullar annobar cutar covid-19 a karamar hukumar ranar Lahadi. Gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, ne ya bayar da umarnin kulle karamar hukumar da yammacin ranar Lahadi. A cikin sanarwar, wacce aka wallafa a shafin sada zumunta (facebook) na gwamnatin jihar jigawa,

an bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne daga karfe 12:00 na safiyar ranar Litinin. Sai dai, a cikin sanarwar, babu wani bayani a kan wanda aka tabbatar da cewa ya kamu da kwayar cutar covid-19 a karamar hukumar. Wannan shine karo na farko da aka sanar da cewa wani mazaunin jihar Jigawa ya kamu da kwayar cutar covid-19. Sannan shine karo na farko da gwamnatin jihar ta sanar da kulle wani gari, ba shiga, ba fita, tun bayan sanar da dokar nesanta da hana taro da rufe ma'aikatun gwamnati.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP



Related Posts

0 Response to "Gwamna Badaru ya kulle karamar hukumar Kazaure bayan bullar annobar covid-19"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?