--
Ganduje ya sasauta dokar kulle a Kano albarkacin watan Ramadana

Ganduje ya sasauta dokar kulle a Kano albarkacin watan Ramadana



Gwamnatin Kano ta sassauta dokar kulle da ta saka a fadin jihar domin dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labari a gidan gwamnatin Kano.

An sassauta dokar ne daga karfe 6:00 na safiyar ranar Juma'a zuwa karfe 12:00 na dare domin bawa jama'a damar yin shirin azumin watan ramadana.

Da ya ke magana amadadin gwamnan jihar Kano, Dakta Gawuna ya ce sassauta dokar ya zama dole domin bawa jama'ar jihar sukunin yin shirin azumin watan Ramadana da aka saba yi kowacce shekara.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a kan dokar kulle da kuma zuwan watan azumi, watau watan 'Ramadan'.

Ya bayyana cewa gwamnatin jiha ta kara wa'adin rufe makarantun jihar har zuwa sanarwa ta gaba.

Ya ce an gwamnati ta dauki wannan mataki ne bisa la'akari da kara yaduwar da annobar cutar covid-19 ke yi a jihar.

Kazalika, ya roki jama'ar Kano su cigaba da bawa gwamnati hadin kai a kokarinta na dakile yaduwar annobar covid-19 a jihar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Related Posts

0 Response to "Ganduje ya sasauta dokar kulle a Kano albarkacin watan Ramadana"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?