
Ganduje ya sallami kwamishinansa da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari
Saturday, 18 April 2020
Comment
- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya sallami kwamishinan ayyuka da gine-gine na jihar, Injiya Mu'azu Magaji
- Hakan ya biyo bayan mummunan furucin da yayi bayan mutuwar marigayi shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari
- Mai bada shawara na musamman ga Gwamna Ganduje ne ya wallafa hakan a shafinsa na twitter
Mai bada shawara na musamman ga Gwamna Ganduje ne ya wallafa hakan a shafinsa na twitter.
Legit.ng ta wallafa cewa, kwamishinan Ayyuka da Gine–Gine na jihar Kano, Muaz Magaji ya yi martani a kan rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari inda ya ce yanzu Najeriya ta samu yanci.
An rantsar da Magaji a matsayin kwamishina ne a ranar 5 ga watan Nuwamban 2O19 ya yi wannan martanin ne a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Asabar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
A baya kwamishinan ya taba wallafa wani rubutu inda ya yi fatan kada Abba Kyari da dawo ya cigaba da ayyukansa a matsayin shugaban maaikatan fadar shugaban kasa bayan ya kamu da Covid-19 makonni kadan da suka gabata.
H.E @GovUmarGanduje has relieved the appointment of the commissioner of Works and Infrastructure, Engr. Mu’azu Magaji with immediate effect.following his unguarded utterances against the person of the late Chief of Staff to the President, Malam Abba Kyari.— Peacock (@dawisu) April 18, 2020
Kwamishinan ya yi kaurin suna wurin yin maganganu a kan alamura da suka shafi abokan adawarsa a siyasa a shafukan sada zumunta wadda hakan ke jan hankalin masu amfani da dandalin sada zumuntar.
A daya daga cikin rubuce rubucen da ya wallafa a Facebook, Mista Magaji ya yi addu'ar Allah ya jikan marigayin amma ya kuma ce, "Nasara Nasara ... Najeriya ta samu yanci kuma Abba Kyari ya mutu a cikin annoba ... Mutuwar shahada in har da Imani mutum ya cika!"
A wani sako daban da ya wallafa a dandalin sada zumuntar ya ce, "Ba za ka iya canja tarihi ba ... Ba abinda zai canja ka, halayen ka sune za su nuna wa duniya ko kai waye ... ko kana raye ko kuma ka mutu!"
KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSA NAN๐๐๐ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y
KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI
Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐๐๐
LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE
KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657
0 Response to "Ganduje ya sallami kwamishinansa da ya yi murnar mutuwar Abba Kyari"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?