--
Farfesa Ayodele Adeleye ya na ikirarin ya gano maganin cutar Corovirus

Farfesa Ayodele Adeleye ya na ikirarin ya gano maganin cutar Corovirus

A Ranar Litinin 13 ga Watan Afrilun 2020, Farfesa Ayodele Adeleye ya fito ya na da’awar cewa ya na da kwayar maganin da ke warkar da cutar COVID-19 da ta addabi Duniya. Ayodele Adeleye wanda kwararren Mai bincike ne ya bayyana cewa kimiyya ta jarraba wannan magani da ya kirkiro, kuma a shirya ya ke ya fara jarraba su a kan Marasa lafiyan.

Adeleye tsohon Malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, kuma ya yi aiki a matsayin Mai bincike a babban asibitin koyarwa na Jami’ar ta Ahmadu Bello Shika, a Kaduna. Farfesan ya shaidawa ‘Yan jarida a wani taron Manema labarai da ya kira jiya cewa ya tabbata wannan magani da ya kirkiro zai warkar da cutar COVID-19 bayan kwanaki uku.

Ya ce: “Idan gwamnati ta kawo mani mutum biyar masu COVID-19, zan warkar da su a gaban ku (‘Yan jarida). Zai dauki kwanaki uku zuwa biyar kafin mai cutar ya warke tsaf.”

Tsohon Masanin Jami’ar ABU Zaria ya ce maganinsa zai warkar da masu COVID-19 Source: UGC Farfesa Adeleye ya ke cewa da wannan magani da ya samo, annobar COVID-19 za ta zama tarihi. Yanzu abin da ake bukata shi ne a samu wadanda za a jarraba maganin a kansu.

“Kusan mutane biyar har da wasu tsofaffin Dalibaina da su ka san ni da bincike su ka rika kira na, su na tambaya ko na samu wani magani da zai iya warkar da cutar COVID-19.” “Wani daga cikin wanda cutar ta kama ya kasance ya na fama da wahalar numfashi, bayan mintuna 10 da shan wannan magani, ya fara samun sauki.” Inji Farfesa Adeleye.

“Mun fada masa ya cigaba da zuwa na kwanaki biyar. Sai mu ka ce masa ya je gwaji, kuma ya samu sauki. Da da shi za mu yi hirar nan, amma shi mutum mai kunyar jama’a ne.”KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN COMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Farfesa Ayodele Adeleye ya na ikirarin ya gano maganin cutar Corovirus "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?