
Enahire: A fito da binciken abin da ke kashe mutane a Jihar Kano – Falana
Tuesday, 28 April 2020
Comment
a Najeriya, ya shaida wannan a wata wasika da ya fitar. Falana ya rubutawa ma’aikatar lafiya takarda, ya na neman mai girma minista Osagie Ehanire ya fito da cikakken rahoton binciken da aka yi. Lauyan ya ba ministan mako guda ne ya yi wannan. Falana SAN ya ce idan aka zarce wannan lokaci ba tare da an fitar da rahoton ba, zai kai gwamnati kotu domin shari’a ta yi halinta. Zai sa a tursasawa gwamnati ta fito da wannan rahoto.
Wannan lauya da ya yi fice ya dogara ne da dokar FOI wanda ta ba shi damar samun duk wani bayani daga gwamnatin kasar. Wasikar ta shiga hannun ministan a karshen makon da ya wuce. Rahotanni daga TVC sun bayyana cewa wannan kungiya ta su Femi Falana ta bukaci a bayyana masu abin da aka gano a binciken da aka yi game da yawan mace-macen da ake yi a jihar Kano.
“Rahoton ya kunshi sila da yanayin mutuwar da ake yi, da adadin wadanda su ka mutu da kuma wadanda su ke jinya a asibitoci, tare da matakan da gwamnatin tarayya ta dauka.” Inji Lauyan. Bayan haka, kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta karbi ragamar shawo kan halin da aka shiga a Kano. Falana da kungiyarsa sun ce lamarin da aka shiga ya fi karfin gwamnatin jihar.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Enahire: A fito da binciken abin da ke kashe mutane a Jihar Kano – Falana"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?