--
Dokar hana fita: Mata a Niger sun rungumi tsarin kayyade iyali

Dokar hana fita: Mata a Niger sun rungumi tsarin kayyade iyali



Wasu matan aure a jihar Niger sun fara tururuwa zuwa asibitoci da cibiyoyin lafiya domin neman magungunan kayyada iyali yayin da gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita a jihar domin takaita yaduwar Covid-19. Mrs Hassana Amos,

mataimakiyar jamiin da ke kula da sashin Bawa Iyali Tallafi a wata cibiyar lafiya a unguwar Limawa a Minna ta bayyana hakan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Amos ta yi wannan jawabin ne yayin wani taron wayar da kai na kwana daya da aka gudanar a cibiyar ta FSP. Ta ce mata da yawa suna ta zuwa cibiyar domin a yi musu allurar sinadarin hana daukan ciki domin gudun daukan juna biyu cikin watanni biyun da za ayi ana zaman gida.

Ta ce, "Muna samun karuwar mutane da ke zuwa wannan cibiyar musamman a ranakun da ake sassauta dokar fita waje a cikin mako.

"Galibin su sun fi son allurar da za ayi musu da zai kiyaye daukan ciki har na watanni biyu. "Sun fi son allurar domin suna ganin hakan zai ba su damar daukan ciki duk lokacin da suke so ba tare da bata lokaci ba." A cewarta, ana kuma yi wa matan gwajegwaje da suka hada da na hawan jini domin a tabbatar za su iya amfani da tsarin kayyade iyalin.

Amos ta kuma kara da cewa baya ga allurar, ana bayar da wasu nauikan magungunan takaita iyali kamar kwayan magunguna na sha, sinadarin saka wa cikin fata da sauransu. Ta ce maza ma suna iya zuwa cibiyar idan suna son takaita iyali su karbi kororon roba. Hajiya Amina Mohammed, daya daga cikin matan da suke zuwa cibiyar ta ce ta tafi ne domin a bata maganin takaita iyali na wata biyu domin ba ta shirya daukan juna biyu ba a yanzu. Ta ce,

 "Miji na maaikacin gwamnati ne kuma yanzu da baya zuwa aiki kullum muna tare a gida. "Hakan na nufin sha'awar mu ta karu. "Ban shirya daukan jiki ba yanzu; shi yasa na ke son yin tsarin takaita iyali yayin dokar hana fitar." Ta ce mijinta ya goyi bayan ta saboda dukkansu ba su amince cewa yanzu suke son haihuwa ba kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

Related Posts

0 Response to "Dokar hana fita: Mata a Niger sun rungumi tsarin kayyade iyali "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?