
Darajar gangar danyen ta sauka zuwa dala 11 a kasuwannin duniya
Monday, 20 April 2020
Comment
Farashin gangar danyen main a kasar Amurka ya yi saukan da bai taba yi ba a shekara 22 a ranar Litinin inda ya karye da kashi 40 zuwa dala 11 sakamakon annobar Coronavirus. Rahoton kamfanin dillancin labaru na AFP yace tun shekarar 1998 rabon da a samu irin wannan karye warwas da farashin gangan danyen mai ya yi a wannan lokaci.
Wani masanin kasuwancin man fetir, Bjornar Tonhaugen ya bayyana dalilin wannan lamari shi ne kasancewar kasashe da dama suna da tarin man fetir a kasa don haka basa bukatar kari. Masanin yace a yanzu haka ba’a amfani da man fetir saboda duniyar ta tsaya cak a dalilin annobar Corona, tun da ba’a amfani da mai, babu bukatar saye, saboda haka mai ya yawaita.
Duk kuwa da matakin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetir, OPEC, ta dauka na rage gangan mai miliyan 10 daga danyen man da ake fitarwa a duk rana, sai da farashin ya karye. Idan za’a tuna a kwanakin baya ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta rage farashin litar man fetir sakamakon karyewar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Gwamnatin ta tsara kasafin kudin shekarar 2020 a kan hasashen farashin gangar danyen mai ba zai yi kasa da $30 ba, saboda shi ne kadai hanyar samun kudin shiga mafi girma a wajenta. A yanzu da farashin danyen man ya karye a duniya zuwa $11, sai dai a zura idanu a ga yadda gwamnati za ta shawo kan matsalolin da hakan ka iya kawo ma tattalin arzikin kasar. A wani labarin, Tsohon minita a jamhuriya ta biyu,
Alhaji Sama’ila Isah Funtua ya shawarci masu danganta shi da mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da su kai kasuwa. Funtua, ya taba zama jami’in mulki a Katsina NA tsawon shekaru 7, ministan ruwa, kuma yana cikin mutanen da suka tsara daftarin kundin tsarin mulki a shekarar 1994-1995. Don haka ya ce baya bukatar wannan muka saboda a cewarsa shi kan sa yana daukan mutane aiki a Najeriya, don haka ya girmi wani ya dauke shi aiki a wannan lokaci.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU BIYOMU A: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP
0 Response to "Darajar gangar danyen ta sauka zuwa dala 11 a kasuwannin duniya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?