--
Dan jarida ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar El-Rufai

Dan jarida ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar El-Rufai



Wani matashin dan jarida, kuma mataimakin mai tace labarai a jaridar Brittle Paper, Otosirieze Obi-Young ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar Gwamna El-Rufai Hadiza isma El-Rufai. Premium Times ta ruwaito Brittle ta sallami Young ne bayan ya yi wani rubutu da yake sukar Hadiza,

bisa zarginta da yake yi da goyon bayan danta da ya yi barazanar yi ma mahaifiyar wani fyade. Shugabar Brittle, Ainehi Edoro ta tabbatar da sallamar.

Young ya tabbatar da sallamar, inda ya bayyana bakin cikinsa bayan kwashe tsawon shekaru hudu yana aiki da kamfanin. Da fari dai rikici ne ya hada yaron Hadiza, Bello, da wani, wanda hakan yasa Bello ya fada ma abokin rikicin nasa bakaken maganganu, wadannan kalamai ne suka sa aka yi masa ca!

Dan jarida ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar El-Rufai a twitter Source: Facebook 

“Ka fada ma babarka, zan yi amfani da ita, kuma har na rage ma abokaina a daren yau. Ban son jin ihun kabilar Ibo.” Inji Bello. Daga cikin wadanda suka ja kunne Bello akwai tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili, wanda ta nemi Bello ya fito ya nemi gafara, amma Bellon ya tsaya kai da fata a kan ra’ayinsa. Wannan ne tasa aka nuna ma babarsa rubutun, amma koda ta gani,

sai ta nuna ba wani abu bane idan Bello ya rama cin mutuncin da wasu ke masa a shafin sadarwa na Twitter. Sai dai daga bisani bayan dogon muhawara, Hadiza ta nemi afuwan jama’a na rashin tsawata ma danta. Da yake sanar da sallamar da aka yi masa, Young yace: “Shugabar kamfanin ta kira ni ta nuna damuwarta da rubutun da nayi da yadda na soki wani kamfanin jaridar Najeriya, sai na gyara rubutun na cire wannan sashin.“

“Ta sake kira na wai za ta sauke rubutun daga shafinsu, ni kuma na ga ba zan iya lamunta ba saboda an hana ni fadan ra’ayina, an sa ni na mayar da ra’ayina kamar wani rahoton labari,“ "Amma duk da haka bai isa ba. Daga nan sai na ce mata ta yi duk abinda za ta yi da rubutun." inji shi. Washe gari Young ya tarar da an hana masa damar shiga shafin yanar gizon kamfanin, an cire shi daga masu kula da shafukan dandalin sadarwar kamfanin, daga nan yasan an sallame shi.

KARANTA WASU LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/




LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇
                            LATSA NAN DOMMIN MAGANA DAMU KAI TSAYE

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

Related Posts

0 Response to "Dan jarida ya rasa aikinsa bayan ya caccaki matar El-Rufai "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?